Rahotanni na cewa yanzu haka kasar Faransa ta fara tattaunawa da sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar kan yiwuwar janye dakarunta daga kasar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke ci gaba da fuskantar matsin lamba na ga fice daga kasar da a baya ta yi wa mulkin mallaka, tun bayan juyin mulkin da aka yi a karshen watan Yulin da ya gabata.
Da yake tabbatar da labarin, tsohon Jakadan Faransa a kasashen Mali da Senegal, Nicholas Normand, ya tabbatar wa gidan talabijin na Aljazeera cewa yanzu haka an fara tattaunawar domin janye wane bangare na dakarun.
Nicholas ya ce wata majiyarsa, wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida masa, ta nuna cewa amma tattaunawar baya nuna Faransar ta amince da halaccin gwamnatin sojin ba.
Sai dai ya ce wani mataki ne na tattaunawa tsakanin sojojin biyu.
Ita ma wata majiya daga Ma’aikatar Tsaron kasar da ta bukaci sakaya sunanta ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ta ce “nan ba da jimawa ba za a fara tattaunawar,” amma ba ta yi karin bayani ba.
Tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Bazoum, gwamnatin Faransar ke takun-saka da sojojin na Nijar saboda ta ki ta amince da gwamnatinsu.
Ko a baya sai da gwamnatin ta bukaci Jakadan kasar da ya fice musu daga kasa, amma ya tsaya kai da fata cewa ba inda zai je.
A yanzu haka dai akwai dakarun Faransa kimanin 1,500 da ke jibge a kasar a shirinsu na yaki da masu ɗauke da makamai a yankin Sahel.
Har yanzu dai ’yan Nijar na ci gaba da zanga-zangar nema sai Faransa ta janye dakarunta daga kasarsu.