✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke zaben Sanatan Kogi

Ta kuma umarci INEC ta sake zabe

Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Kogi ta soke zaben Sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Isah (Echocho) tare da umartar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sake sabon zabe.

Sanatan da aka soke zaben nasa dai shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai Mai kula da harkokin Hukumar Kwastam.

Hukuncin ya biyo bayan soke sakamako a mazabu 94 ne na mazabar.

Shugaban kotun, Mai Shari’a K.A. Orjiako, ne ya yanke hukuncin yayin zaman kotun ranar Talata.

Hakan dai ya biyo bayan karar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, Dokta Victor Adoji, ya shigar a gaban kotun ta hannun lauyansa, Johnson Usman (SAN), yana kalubalantar yadda aka bayyana wanda ya lashe shi duk da cewa kuri’in da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin ’yan takarar guda biyu.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun ya amince da korafin mai kara, inda ya soke nasarar Da Sanatan mai ci ya samu tare da bayar da umarnin janye takardar shaidar lashe zaben.