✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rusa duk shagunan da aka gina a filayen makarantun Oyo – Makinde

Ya ce an gina makarantun ne domin karatu, amma ana neman mayar da su kasuwa

Gwamna Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayar da umarnin rusa dukkan shagunan da aka gina a cikin harabobin makarantun gwamnati da ke Jihar.

Gwamnan wanda ya jagoranci wasu Kwamishinoninsa zuwa ziyarar gani da ido na irin wadannan makarantu a Ibadan da safiyar Talata ya ba su wa’adin kwana 7 su tattara komatsansu daga harabobin makarantun.

Ya ce an samar da makarantun ne domin ilimantar da yara amma masu shagunan suke neman mayar da su kasuwanni.

A wani labarin kuma, Gwamnan ya bayar da umarnin rufe wasu bankunan kasuwanci da kamfanonin sadarwa yin saboda kunnen kashi wajen biyan kudin harajin wuraren da suke zaune.

Da yake bayar da umarnin rufe wuraren, Darakta a Ma’aikatar Gidaje da Tsare tsare ta Jihar, Olufisayo Ogunbiyi ya ce kafin a dauki matakin rufe wadannan bankuna da kamfanonin sadarwa sai da aka sanar da su tare da ba su wa’adi a kan irin matakan da za a dauka a kan su idan suka ki yin aiki da wannan umarni.