Fararan da kawayenta na kasashen Tururai sun sanar da janye dakarunsu da suka girke a kasar Mali a ranar Laraba.
Hakan na zuwa ne a yayin da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ke kai ziyarar aiki ta kwana biyu a birnin Brussels na kasar Belgium dangane da aikin dakarun a yankin Sahel.
- ‘’Ku kuka da kanku idan aka sake kashe dan Arewa a Kudu’
- Abba Kyari ya ce ’yan IPOB ne suka kulla masa sharri
Sojojin rundunar Barkhane ta Faransa da takwarorinsu na Takuba na kasashen Turai da na kasar Burkina Faso sun shafe kimanin shekara 10 a Mali suna taimaka wa dakarun kasar wajen yakar mayakan Jihadi.
Rundunar ta ce, “Sun yanke shawarar janye sojojinsu da kayan soji da ke yankin kasar Mali.”
Tun lokacin da aka fara girke dakarun rundunar Barkhane na Faransa a yankin Sahel, sun yi ta fama da matsaloli, inda aka kashe 53 daga cikinsu.
A 2013 ne dai Faransa ta fara girke sojojinta a Mali domin yakar masu tayar da kayar baya, amma har yanzu haka ba ta cim-ma ruwa ba.
Sai dai sun ce ko sun janye daga Mali, za su ci gaba da da aiki a sauran kasashen Sahel, ciki har da Jamhuriyar Nijar a yankin Tekun Guinea.