Wasu Falasdinawa sun ce za su maka kasar Isra’ila a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) kan yadda Yahudawa ke ci gaba da mamaye matsugunansu, musamman a birnin Kudus.
Ko a cikin makon nan dai, akalla mutum tara da wasu ’yan jarida ne jami’an tsaron Isra’ilan suka kai wa hari bayan sun rushe musu gida mai hawa biyu a Karameh, wani kauyen da ke wajen birnin Kudus, saboda zarginsu da ‘yin gini ba bisa ka’ida ba’.
- ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso saboda juyin mulkin sojoji
- An kama soja yana fashi da makami a Yobe
Akalla dai iyali mai mutum 15 ne aka kora daga gidan ta karfin tsiya, aka kuma jikkata wasu mutum shida yayin samamen da ’yan sandan Isra’ila suka jagoranta, kamar yadda kungiyar bayar da agaji da Red Crescent a kasar ta tabbatar.
To sai dai wani iyali da ake kira Salhiyeh, ya ce zai maka Isra’ilan gaban kotun ICC, bayan an fitar da su daga gidansu da ke unguwar Sheikh Jarrah a Gabashin birnin na Kudus, kafin daga bisani kuma a rusa shi.
“Babu adalci a abin da Isra’ila take yi a kasata sam, sun lalata min rayuwa,” inji Lital Salhiyeh, mai kimanin shekara 40, yayin hirarta da gidan talabijin na Aljazeera.
A cikin makon da ya gabata, mijin Lital, Mahmoud da ’ya’yansu da dama sai da suka gudanar da wata zanga-zanga a kan saman rufin dakinsu, suna barazanar hallaka kansu da tukunyar gas muddin aka yi kokarin fitar da su daga gidan nasu da suka shafe tsawon shekaru a cikinsa.
Sai dai bayan ’yan kwanaki, dakarun Isra’ila sun yi wa gidan nasu kawanya, suka kama su sannan suka lakada musu duka.
Daga bisani dai an kai su gidan yari inda suka zauna tsawon kwanaki, kafin daga baya lauyansu ya karbo belinsu.
A bisa dokokin kasa da kasa dai, mamayar da Isra’ila take a gabar Yammacin Kogin Jordan kan matsugunan Falasdinawa haramtacciya ce, saboda ta saba da tanade-tanaden yarjejeniyoyin Geneva ta 1949 da ta Rome ta 1998.