✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Falasdinawa sun rufe makarantu saboda matsin lambar Isra’ila

A yanzu da akwai sama da makarantun Falasdinawa 280 a birnin Jerusalam.

Daruruwan makarantu ne ke rufe a yankunan Falasdinawa wacce Isra’ila ta mamaye sakamakon wani bore da malamai da kuma iyaye ke yi na kin yunkurin Isra’ila na sauya tsarin ilimi a kasar.

Rufe makarantun ya biyo bayan yunkurin hukumomin kasar Isra’ila da suka ce abin da ake koyawa yara a makarantun yakunan Falasdinawa, da kuma tilasta musu amfani da wani tsari na daban da Isra’ilan ta samar.

Rufe makarantun a ranar Litinin na cikin jerin matakan da iyayen Falasdinawa suka dauka na tsawon mako guda don nuna rashin amincewarsu da kudurin na Isra’ila.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa ta hadin gwiwa a hadaddiyar kungiyar kwamitin iyayen yara da kuma kungiyar ‘yan gwagwarmaya ta Islama suka fitar a Jerusalam a ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun yi kiran shiga yajin aikin gama gari na malmai, da kuma kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su sa baki cikin lamarin don ceto makomar tsarin ilimin Falasdinawa.

‘Yan jarida da kuma sauran mutanen gari na ta rarraba hotunan azuzuwan makarantun da suka kasance babu kowa a ciki a ranar ta Litinin domin jan hankalin duniya.

Shugaban kwamitin iyayen yaran, Ziad al-Shamali, a hirarsa da Al Jazeera na cewa, idan yunkurin Isra’ila ya samu nasara, hakan zai sa ta samu juya akalar kashi 90 na ilimin daliban birnin Jerusalam.

“A yanzu da akwai sama da makarantun Falasdinawa 280 a birnin Jerusalam da kuma dalibai 115,000 daga nozari zuwa sakandire,” in ji Ziad.

A cewar Al shamali, kimanin kashi 90 zuwa 95 ne na wadannan makarantun ke a rufe sakamkon yajin aikin kin amincewa da tsarin na Isra’ila.