✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalu dorayi ya caccaki ’yan siyasa da jami’an tsaro kan kashe-kashe a Zamfara

Fitaccen darakta kuma jarumi a masana’antar fina-finan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood, Falalu dorayi ya caccaki shugabanni kan sakacin da suke nunawa dangane…

Fitaccen darakta kuma jarumi a masana’antar fina-finan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood, Falalu dorayi ya caccaki shugabanni kan sakacin da suke nunawa dangane da kashe-kashen da aka yi a Arewacin kasar nan musamman ma a Jihar Zamfara.

Darakta a cikin wata mukala da ya rubuta wadda ya yi mata take da ‘Ta’addanci: Sara Suka ko ’Yan Shara’ yabukaci jagorori su tashi tsaye wajen ganin an magance kashe-kashen da suke aukuwa a kasar nan.

Ya ce, duk lokacin da adalci ya yi karanci a cikin al’umma, sannan jagorori ta ko wanne fanni suka fifita bukatarsu da ta matansu da kuma ’ya’yansu a kan ta al’ummar da suke yi wa jagoranci, to al’umma za ta kasance mara imani da tausayi.

“A yanzu ya zamo burin dan Adam ya zalinci dan uwansa. Wasu su kwashe abinci su boye sai ya yi tsada su fito da shi. Wasu su dauki makamai su dinga kai hare-hare kan ’yan uwansu. Hakan rashin imani ne,” inji shi.

Ya ce, dole ne sarakuna da malamai da ’yan siyasa da jami’an tsaro da kuma jama’ar kasar nan su tashi tsaye don ganin an kawo karshen hare-haren da ake kai wa kan jama’a.

Ya ce “Mallakar muggan makamai a hannun ’yan ta’adda da ke #ZAMFARA, inda hakan yake haifar da kisan kiyashi mara adadi zalunci ne, kuma abin takaici ana kallo ana nema a mayar da lamarin na siyasa, don zalunci, domin idan ba zalunci ba ina ake siyasa da rayukan al’umma.”

Ya kara da cewa, sara-suka ko ’yan daba inda wasu matasa ke amfani da wukake a jihohinmu na #AREWA suna bin unguwanni suna saran duk wanda tsautsayi ya afkawa abin takaici ne, inda kuma wasu suke aikata hakan domin bukatar kansu ko kuma don bukatar iyayen gidansu.

Ya jaddada cewa lallai ya kamata a tashi tsaye a kan wannan matsala, domin barin ta tana ci gaba barazana ne ga zaman lafiya, domin duk mai hankali ya san duk fitina da tashin hankali a haka suke farawa har su gagari gwamnati da kuma al’umma. 

Ya ce, “An gaya mana babu wata shekara face mai biye mata ta fi ta sharri, har sai mun koma ga Ubangijinmu.”