✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalar Watan Ramadan Ga Ma’aurata

Assalamu Alaikum ma’abota bibiyar wannan fill na iyayen giji mai tarin albarka. Ya ya ibada? Allah Ya karba mana kuma Ya sanya mu cikin ‘yantattun…

Assalamu Alaikum ma’abota bibiyar wannan fill na iyayen giji mai tarin albarka.

Ya ya ibada? Allah Ya karba mana kuma Ya sanya mu cikin ‘yantattun bayi.

A yau zan yi tsokaci a kan yadda uwargida yakamata ta zage damtse a cikin wannan wata mai alfarma don gamsar da mijinta da yara da sauran al’umma makusanta.

Abin da ya sa na kawo wannan maudi’in shi ne kasancewar uwargida na da gagarumin aiki a kurarren lokaci wanda in aka samu uwargida mai kasala za ka ga ta kasa amfani da sa’oin da take da shi wajen gudanar da ayyukanta na ibada da na cikin gida.

A nan zan warewa uwargida lokuttan da ya kamata a ce tun kafin shigowar wannan wata na Ramadan ta tanade su wanda ko shakka babu zai taimaka mata.

Zan kasa mata lokutta zuwa kashi hudu kamar haka;

1- Lokacin hutawa; duk da a wannan wata ya kamata ya kasance kankane matuka,

2- Lokacin ibada wanda ya hada da kiyaye lokuttan daukar azumin da buda baki, sallar tarawihi da tahajjud, karatun Kur’ani da zikirorin safe da yamma da sauran su.

3- Lokacin ayyukan gida da kula da yara,kamar dafuwar abinci da hada kayan buda baki da sahur, gyaran gida, da sauran su.

4- Lokacin kula da maigida, wajibi ne ga uwargida ta kula da lokuttan da maigida yake zuwa aiki ta hanyar tashi da wuri ta fara gyara kanta da cikin gida sannan ta hada masa ruwan wanka ta fitar masa da kayan da zai sanya sannan ta tabbatar ya kimtsa sannan ta raka shi ta yi masa ban kwana.

A nan kar uwargida ta kasance ta shantake ba ta ma san maigidan ya fita ba.

Dalilin da ya sanya na rabawa uwargida lokuta kamar haka shi ne, in muka duba kamar yadda na fada akwai karancin sa’oi’n da muke da su ga kuma tarin ayyuka wanda in har uwargida ba ta kiyaye ba ko shakka babu zai yi wuya ta cinma hakarta kafin faduwar rana zuwa fitowar alfijir.

 

MAIGIDA DA GUDUNMUWARSA A WANNAN WATA.

 

Ko shakka babu uwargida ita kadai ba ta iya cikawa tare da kiyaye wadannan sharudda da lokutta sai da taimakon maigida.

Maigida na da gudunmuwa kamar haka;

1- Ya taimaka mata wajen kiyaye lokuttan da za ta tashi don gabatar da ibada ko ayyukan gida.

2- Bude bakin aljihu domin shirya kayan bude baki da sauran kayayyakin makwalashe domin kuwa ana bukatar a yalwata gami da cin abubuwa masu dadi a wannan wata.

3- Ta da uwargida da sauran yaran gida don yin ibada kamar sallar dare da karatun Kur’ani.

 

FALALAR WATAN RAMADAN:

Kamar yadda muka sani, wannan wata ne mai alfarma watan da aka saukar da Alkur’ani a ciki, sannan wata ne da ake son ciyar da mabukata kuma a karshen sa akwai wani dare wanda in mutum ya dace da daren yana ibada a ciki ya fi ibadar wata dubu, kuma Allah na ’yanta bayin sa daga wuta.

Da fatan uwargida da maigida za su zage damtse don dacewa da romon da Allah Ya tanadar wa masu tsayawa a wannan wata.

Sanusi Hashim Abban Sultana

Daga Jihar Katsina

08065507271

[email protected]