Da sunan Allah, Mai tausayi, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin bayinSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi Balarabe, tare da alayensa da sahabbansa, masu daraja.
Bayan haka, in mai karatu yana biye da mu zai ga tsokacin namu ya kai karshen yadda ake alwala cikakkiya da yadda aka fara gabatar da falala da fa’idojinta, to yau ga karashen mukalar. Allah Ya sa mu yi muwafaka da alheran da ke ciki:
2(a) Haka nan an samo hadisi daga Usman, (Allah Ya yarda da shi), Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Wanda duk ya yi alwala – kamar haka (ya nuna yadda alwalar take a aikace) – an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa, kuma sai sallarsa da tafiyarsa zuwa masallaci ta kasance nafila.” Imam Muslim (229) da waninsa suka fitar da shi.
Malam ya ce: “Wannan falala tana samun karin karfi da kuma lada ga wanda ya yi Sallah ta farilla ko nafila bayan ya kammala wannan alwalar, kamar yadda ya zo:
(b) A cikin Hadisin Usman – cikin siffar alwalar Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya yi alwala, kwatankwacin alwalata wannan, sannan ya tashi ya yi Sallah raka’a biyu, bai yi wani zancen zuci ba, an gafarta masa abin da ya gabatar na zunubansa.” Imam Buhari (6433) da Imam Muslim (226) da waninsu suka fitar da shi.
Na uku: Yana daga cikin fa’idojin alwala, ta kasance daukakar daraja ce ga bawa Musulmi. An samo daga Abu Huraira, (Allah Ya kara masa yarda), Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Shin ba na shiryar da ku ba, ga abin da Allah Zai kankare muku zunubai da shi, kuma darajojinku su daukaka?” Sai (sahabbai) suka ce, “Eh, muna so, ya Ma’aikin Allah!” Sai ya ce, “Ku kai matuka wajen cika alwala, a lokutan matsi (kamar lokacin sanyi – misali) da yawaita tattaki zuwa masallaci da zaman-jiran Sallah, bayan an kare wata (Sallar), wannan kuwa shi ne ribadi, wannan kuwa shi ne ribadi, wannan kuwa shi ne ribadi.” Imam Muslim (251) da waninsa suka fitar da shi. (Ribadi – shi ne zaman dako, wajen kare Musulmi da daukaka matsayin Musulunci).
Na hudu: Yana daga cikin fa’idojin alwala, cewa ita hanya ce zuwa Aljanna:
(a) An samo Hadisi daga Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce wa Bilal, (Allah Ya yarda da shi), “Ya Bilaal! Ba ni labari da wani aiki da ya fi soyuwa gare ka da ka aikata a Musulunci, saboda ni na ji motsin takun takalmanka a gaba gare ni a cikin Aljanna!” Sai (Bilal) ya ce, “Ban aikata wani aiki ba, wanda ya fi soyuwa gare ni, kamar yadda ban taba yin alwala, a kowane lokaci na dare ko rana ba, face na yi Sallah da wannan alwala, abin da Allah Ya so in salla ta.” Imam Buhari (1149) da Imam Muslim (2458) suka fitar da shi.
(b) An samo daga Ukbata dan Amir, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Na ji Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Duk wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata ta, sannan ya sallaci raka’a biyu, alhali ya fuskance ta da zuciyarsa, Aljanna ta wajaba gare shi.” Imam Muslim (234) da Annasa’i (80/1) da waninsu suka fitar da shi.
Na biyar: Yana daga cikin fa’idojin alwala, cewa ita wata alama ce ta rarrabewa tsakanin wannan al’umma ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), wajen da ake gangarawa zuwa Tafkinsa, (Sallallahu alaihi wasallam), a lahira.
An samo daga Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), cewa Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya je makabarta, sai ya yi musu sallama – ya karanta abin da akan karanta in an je makabarta wanda ke da ma’anar “Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku (da ke gidan) jama’ar muminai, mu ma in Allah Ya so, (masu risker ku ne), nan ba da dadewa ba, masu haduwa ne.” Na yi kwadayi da dai mu, lallai, mun ga ’yan uwanmu.” Sai (sahabbai) suka ce, “Ashe mu ba ’yan uwanka ba ne ya Manzon Allah?” Sai ya ce, “Ai ku sahabbaina ne, kuma ’yan uwanmu su ne wadanda ba su zo ba, sai daga baya.” Sai suka ce, “Yaya za ka gane wadanda ba su zo ba, na daga al’ummarka ya Ma’aikin Allah?” Ya ce, “Ba ka gani ba, abin a ce mutum yana da rakumansa danda-danda a tsakanin sauran rakuma, ba zai iya gane rakumansa ba?” Suka ce, “Lallai zai gane ya Manzon Allah.” Sai ya ce, “To, a haka, saboda su (al’ummata) za su zo danda-danda daga (gurabun) alwala, alhalin ni ina jiransu a gefen tafki. Ku saurara! (Zan ga) ana kore wasu mutane, kamar yadda ake kore rakuman da ba su cikin garke (wadanda suka yi batan-kai zuwa cikin wani garke), sai in kasance ina kiran su (mutanen da ake korewa daga tafkin) ina cewa ‘ku taho nan,’ sai a rika cewa, “Lallai su, sun baddala al’amari (na ibada ba kamar yadda ka koyar ba) a bayanka.” Ni kuma sai in ce “Nesa! Nesa! (wato a yi nesa da su daga nan).” Imam Muslim (234) da Annasa’i (80/1) suka fitar da shi.
Malam (Abu Malik) ya ce, “Abin da ake nufi da ‘gurrah’ shi ne wata alama fara da kan kasance a goshin doki. Amma abin nufi a nan (wurin alamomin alwala) shi ne haske mai kasancewa a fuskokin al’ummar Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam). Kuma abin da yake ‘attahajiil’ shi ne farin da ke wurare uku na kafafun doki din. Nan ma abin da ake nufi shi ne haske (a wurin da akan wanke na alwala) na kafafu da hannaye, wadanda gaba daya ake cewa danda-danda. Allah Shi ne mafi sani. (Bayani kamar yadda aka fitar a Sharhin Muslim na Imamu Nawawi, 100/3).
Na shida: Yana daga cikin falala da fa’idojin alwala kasancewarta haske ga bawa Musulmi Ranar Alkiyama. Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), ya ce “Na ji Khalilina (abokina, Ma’aiki), (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Hulyah (haske Ranar Alkiyama) yana kaiwa matuka daga muminai ta fuskar da alwala ta kai matuka (wato ta cika).” Imam Muslim (250) da Annasa’i (80/1) suka fitar da shi.
Na bakwai: Yana daga cikin falala da fa’idojin alwala kasancewarta abin kwance kullin shaidan. An samo daga Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Shaidan yana yin kulli uku a keyar dayanku, idan kuna barci, sai ya rika bugun kowane kulli yana fadin, ‘dare yana da tsawo, saboda haka yi ta barcinka.’ Idan (dayanku) ya farka kuma ya ambaci Allah, sai kulli daya ya kwance. Idan kuma ya yi alwala, sai daya kullin ya kwance. Idan ya yi Sallah, sai daya kullin (na uku) ya kwance. Sai ya wayi gari cikin nishadi tare da walwalar zuciya (cikin farin ciki). In kuwa haka ba ta samu ba, sai ya wayi gari cikin kaushin zuciya, yana mai kasala.” Imam Buhari (1142) da Imam Muslim (776) suka fitar da shi.
Wannan shi ne karshen abin da Malam ya kawo dangane da falala da fa’idojin alwala. Allah Ya sa mu dace da su, duniya da Lahira. Allah Ya sa karshenmu ya yi kyau, amin.