Pope Francis ya bayyana damuwa kan abin da ya kira ‘mugun’ hadin baki a tsakanin Amurka da Rasha, inda ya ce shugabannin biyu suna daga cikin wadanda suka ‘jirkita ma’anar duniya,’ idan aka zo batun ’yan gudun hijira. |
Fafaroman ya bayyana haka ne a tattaunawa da wata jaridar kasar Italiya a ranar Alhamis din makon jiya inda ya caccaki hadin bakin kasashen biyu da ta China da Koriya ta Arewa da kuma Rasha da Siriya a daidai lokacin da manyan shugabannin duniya suke halartar taron kasashe 20 masu arziki na duniya a kasar Jamus.
“Na damu da mugun hadin baki a tsakanin manyan kasashen biyu da suka jirkita manufar duniya: Amurka da Rasha da China da Koriya ta Arewa (Shugaban Rasha Bladimir) Putin da (na Siriya Bashar) Assad kan yakin da ke gudana a Siriya,” Fafaroma ya shaida wa jaridar La Repubblica.
“Hadarin ya shafi gudun hijira,” inji Fafaroma kamar yadda kafar labarai ta AFP ta fassara. “Babba, kuma matsala mafi daga hankali da ke habaka a duniya a yau ita ce, an yi watsi da matalauta da masu rauni, ciki har da ’yan gudun hijira,” inji shi.
Gargadin ya zo ne kwana daya kafin Shugaba Donald Trump ya yi ganawar gaba-da-gaba ta farko da Shugaban Rasha Bladimir Putin
Taron da aka shirya zai gudana a cikin minti 30, shugabannin biyu sun shafe awanni suna ta yabon juna.
Fafaroma ya sha nuna damuwa kan yadda Rasha ta mayar da yankin Kiremiya da ke kasar Ukraine wani bangare na kasarta, kuma ya sha sukar Shugaba Trump kan matsayinsa na kyamar baki, inda a wani lokaci ya ce Trump “ba Kirista ba ne,” bayan da Shugaban ya yi yunkurin gina katanga a kan iyakar kasar.
“Masu gudun hijira ’yan uwanmu ne da suke neman rayuwa mai kyau, wadda ta yi nesa da talauci da yunwa da kuma yaki,” Fafaroma ya sake rubutawa a shafinsa na tiwita a ranar Asabar da ta gabata.