Shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Shettima a Jam’iyyar APC, Simon Lalong, ya ce yana alfahari da mukaminsa a matsayinsa na cikakken Kirista.
Ya ce a matsayinsa na Kirista dan darikar Katolika kuma wanda aka yi wa Baftisma, ya yarda ya jagoranci yakin neman zaben shugaban kasa da mataimakinsa Musulmai saboda addininsa bai hana ba.
Gwamanan Jihar Filaton ya ce yana shakkun imanin Kiristocin da ke sukar shi don ya karbi jagorancin yakin neman zaben Tinubu da Shettima saboda su Musulumi ne.
Laong ya ce je makarantun ’yan mishon kuma yana da lambar yabo mai girma daga fafaroma kuma har yanzu, “Muna ganawarmu ta ibada da fafaroma da dare.
“Duk abin da muke yi, da shawarwarinsa muke yi, amma bai ce kar na karbi wannan mukami ba, don haka abin da ya fada shi za mu yi,” inji shi.
Ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarifa a Abuja bayan ganawarsa da Shugaba Buhari a ranar Laraba.
Ya kara da cewa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Filato da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon duk sun zo tarbar sa a filin jirgin saman Jos, wanda haka ya nuna cewa mutanensa na tare da shi.
Don haka a cewarsa, yana shakkun imanin Kiristocin da ke sukar shi don ya karbi jagorancin yakin neman zaben Musulmi.