Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Kano ta soke hukuncin Kotun Musulunci kan rabon gadon Marigayi Manjo Mohammed Arogun Adeniyi.
Marigayi Manjo Mohammed Arogun AdeniyiM daga Jihar Kwara ya rasu ne a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, kuma an yi jana’izawar bisa tsarin addinin Islama.
Tsohon hafsan sojan ya rasu ya bar mahafainsa, da matasa uku, Muusulmi biyu, Maimuna da Inna Fatima da kuma Kirista daya, Evangelist Olabisi da kuma ’yarta Nike.
Bayan rasuwarsa ne Rundunar Sojin Najeriya ta biya hakkinsa Naira miliyan 23.59 ga ’yarsa Nike, wadda ke matsayin mai gadonsa.
- Gwamnatin Tinubu ba ta da alkibla —Atiku
- Matashi ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu
- ’Yan Najeriya miliyan 31.8 na fuskantar ƙarancin abinci — Rahoto
Rikici ya barke ne bayan da Nike ta hana sauran matan kasonsu daga kudin gadon, lamarin da ya sa suka kai lamarin kotu Babbar Kotun yanki ta daya da ke Ilorin, kuma suka samu nasara.
Amma Nike da mahaifiyarta, Evangelist (Mrs.) Olabisi Mohammed, suka garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara ta Musulunci, cewa da Dokar Aure ta Jihar Kwara aka daura musu aure kuma ita ya kamata a bi wajen rabon gadon mamacin.
Sun bayyana cewa Dokar Rabon Fadon Jihar Kwara ta wajabta amfani Dokar Auren jihar, gami da haramta amfani da Shari’ar Musulunci wajen rabon gadon mamacin.
Daga karashe Kotun Daukaka Karar Musuluncin karkashin jagoranin Mai Shari’a Lawan Shuaibu, ta soke hukuncin babbar kotun yankin, da cewa a yi amfani da dokar auren jihar wajen rabon gadon.
Sai dai ta kara da cewa duk mutumin da ya rayu har ya bar duniya a bisa Musulunci, wajibi ne bin Musulunci wajen rabon gadonsa, domin a fili yake cewa Musulmi ne.
Alkalan sun bayyana cewa duk da cewa Manjo Mohammed ya auri Kirista, hakan bai fitar da si daga Musulmi ba.
Hasalima Muusulunci ya halasta auren fiye da mace daya da kuma Kirista, haka kuma yana da ’yancin yin hakan a bisa kundin tsarin mulkin Najeriya.