✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faduwar darajar Dala: ’Yan canji sun koka

’Yan kasuwa da ke hada-hadar canji kudin kasashen waje sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da matakin da bankuna suka dauka na kin karbar ajiyar…

’Yan kasuwa da ke hada-hadar canji kudin kasashen waje sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da matakin da bankuna suka dauka na kin karbar ajiyar Dala daga ’yan kasuwa inda hakan ya daga darajar naira. 

A farkon makon nan darajar Naira ta daga inda ake sayan Dala a kan Naira 215, inda a kasuwar bayan fage ake sayar da ita a kan Naira 217 zuwa Naira 218.
Amma a ranar Talatar makon jiya, ana sayar da Dala a kan naira 220 zuwa 225 a sayar da ita Naira 230 zuwa Naira 240.
Wani dan canji da ke harka a Jihar Legas, Alhaji Auwalu Azare ya shaida wa Aminiya ta wayar salula cewa matakin da bankunan suka dauka ya janyo musu asara mai yawa.
Ya ce: “Gaskiya ba mu ji dadin matakin da bankunan suka dauka ba. Saboda mutane da yawa sun yi asara mai yawa saboda babu inda za su tura kudi ko kuma su karba. Saboda kusan ita ce hanya daya tilo da masu harkar canji suka dogara da ita wajen tura kudi da kuma karba. Saboda haka idan babban bankin Najeriya bai dauki mataki ba na samar da wata hanya da za mu rika tura kudi, mutane da yawa za su karye.”
Shi ma Alhaji Musa Sakkwato wani wanda ke harkar canji cewa ya yi lamarin ya jefa su cikin kaka-ni-kayi.
“Matakin da bankuna suka dauka bai yi mana dadi ba don gaskiya mun yi asara mai yawa wasu daga cikinmu sun rasa kwastominmu. Saboda haka muna kira gare su da su tallafa mana su bar mu mu rika biyan kudi ta asusun ajiyarmu,” inji shi.
A watan da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya wato CBN ya dakatar da bai wa masu shigo da kaya Dala don bankin ya ririta ajiyar da yake da ita.
Hakan ya janyo manyan kamfanonin da ke shigo da kaya sun sayi Dala daga kasuwannin bayan fage, inda suka ajiye a asusunsu don tura wa kasashen waje.
Daga bisani sai babban banki ya umarci bankuna su dakatar da karbar Dala daga hannun masu ajiya. Wannan ya janyo darajar Dala ta fadi farashin naira ya daga.