Magoya bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun bayyana cewa kayen da jam’iyyar APC ta sh a zaben gwamnan Jihar Osun ba zai sa su karaya ba.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Shugaban magoya bayan Tinubu na kasa, Kwamared AbdulHakeem Adegoke Alawuje, ya bukaci dukkanin magoya bayan Tinubu a kan kada sakamakon zaben ya girgiza su.
- NAJERIYA A YAU: PDP Ta Yi Waje Da APC A Osun
- ’Yan kwadago za su yi zanga-zangar kwana 2 don goyon bayan ASUU
“Babu dalilin da zai sa mu bata lokacinmu wajen yin nadama kan abin da ya faru a Osun, mu dai kawai mu gyara tafiyarmu,” in ji Alawuje.
Ya kuma jaddada bukatar magoya bayan Tinubu su koma kan teburin tsarin yakin neman lashe zaben shugaban kasa na 2023 ga Tinubu.
“Dole ne zaben Osun ya zama bai damu kowa ba, darasi ne mai kyau da ya kamata ya sa mu gyara gaba.
“Ina kuma kira ga wadanda suke jagororin kungiyar yakin neman zaben Tinubu da kada su yi kasa a guiwa saboda abin da ya faru.
“Gaskiya daya ce wadda ba ta wuce amfani da kabilanci da addini da abokan hamayyar Tinubu suke fakewa da su ba.
“Mu kwantar da hankalinmu sannan mu don bude idanunmu don gano nagartar ’yan takara, mene ne tarihinsu na baya da suka ajiye sannan mu ajiye siyasa a gefe.
“Matsala daya tilo da muke da ita a Najeriya ita ce, mun ki gano bambance-bambancen daidaikun mutane, muna kokarin yin watsi da su. Amma tsari na rayuwa ba zai sa hakan ta faru ba, yana da kyau a nemo mafita ba tare da an tauye wa wani hakkinsa ba.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su gane cewa idan muka yi zabe bisa dalilai na hankali, to duk wanda ya lashe zaben zai dauki lokaci kafin ya sauka a sake zabar wani, don haka a yi zabe da hankali.
“Abin da ya kamata mu lura shi ne shugabanci nagari, yadda za mu samu jagorori da za su yi aiki ga kowa da kowa, yadda za mu inganta ayyukanmu na kasa, da yadda za mu ciyar da tsarin tattalin arzikinmu gaba da dai sauransu,” a cewarsa.