✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadawa ne suka kewaye Buhari – Akibishop Kaigama

A makon da jiya ka jagoranci Bishop-Bishop na zuwa fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda kuka gana da shi, me ya kai ku fadar? Mun…

A makon da jiya ka jagoranci Bishop-Bishop na zuwa fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda kuka gana da shi, me ya kai ku fadar?

Mun je fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, don mu gana da shi kamar yadda muka saba. Domin tun kafin ya zama Shugaban kasa, wato lokacin da yake yakin neman zabe, mun je mun gana da shi, mun tattauna da shi kan abubuwa da dama da suka shafi kasarmu da rayuwar al’ummar Najeriya baki daya. Lokacin da ya zama Shugaban kasa ma mun kai masa irin wannan ziyara. Wato a takaice wannan ziyara da muka kai wa Shugaban kasa ita ce ta uku, kuma mun kai masa wannan ziyara ce, domin mu tabbatar masa cewa muna goyan bayansa, muna yi masa addu’ar Allah Ya ba shi nasara a kan shugabanci da yake yi wa Najeriya da al’ummar Najeriya baki daya. 

Bayan haka mun mika masa koke-koke da matsalolin da suke damun al’ummar Najeriya, domin muna aiki da jama’a ne a kasa, wato mutanen da suke zaune a yankunan karkara, inda talakawa suke zaune. Don haka muka ce bari mu je mu bayyana masa irin wadannan koke-koke da talakawa suke yi, kuma mu ba shi shawara kan yadda za a samu a gyara wadannan matsaloli da suke damun talakawa. Domin babu shakka akwai matsalolin talauci da rikice-rikicen da suke kawo asarar rayukan al’umma da matasa masu shaye- shayen miyagun kwayoyi da masu son tayar da rikice-rikice da rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma da sauransu. Wato akwai abubuwa da yawa da suke damun kasar nan, da ya kamata mu taru mu yi aikin gayya wajen ganin mun magance su. 

Bisa koyarwar addinin Kirista an gargade mu kan mu bai wa kowane shugaba goyon baya, kuma mu yi masa addu’a. Domin duk wanda aka ce shugaba ne, Allah ne Ya zabe shi Ya ba shi shugabanci don ya taimaki al’umma. Saboda haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari Allah ne Ya zabe shi ya ba shi shugabancin Najeriya. Akwai aiki a kanmu mu taya shi da addu’a kuma mu ba shi shawarwari masu kyau. Mu gaya masa inda matsala take domin shi uba ne na kasa baki daya. Kuma ya kamata idan abu yana tafiya daidai ya sani, idan abu ba ya tafiya daidai ya sani.

Amma yawaicin mutane musamman masu aiki kusa da Shugaban kasa, ba sa gaya masa gaskiya, sai abin da yake son ya ji ne suke fada masa, abin da ba gaskiya ba, sai su fada masa. Musamman ganin cewa har yanzu a kasar nan, muna fama da matsalar wutar lantarki. Wasu wurare babu ruwan sha, yara da yawa suna zuwa ofishina neman taimako. A yau din nan na samu wasiku da dama na matasa da mata da suke neman taimakon zuwa asibiti da abinci da kudin hayar gida da kudin jarrabawa da sauransu. 

Don haka yana da kyau a rika gaya wa Shugaban kasa gaskiya, abin da ya kai mu wajen Shugaban kasa ke nan. Muka ce ba za mu rude shi ba, akwai cigaba a gwamnatinsa, misali kamar yaki da Boko Haram da yaki da cin hanci da rashawa babu shakka yana kokari a wadannan bangarori. Amma akwai batagari da ba sa son irin wannan ci gaba da ake samu a Najeriya, don haka muka gaya masa cewa ya kara bode ido. Ya tashi ya kara kokari, domin akwai abubuwa da dama da ya kamata ya duba, in ya yi haka za a kara samun nasara a wannan gwamnati.

Wadansu fitattun ’yan Najeriya suna shawartar Shugaban kasa Buhari cewa kada ya sake tsayawa takara a zaben badi me za ka ce kan wannan magana?

Masu kawo wannan shawara ba su san cewa kundin tsarin mulkin kasar nan, ya bai wa Shugaba Buhari damar ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben badi ba ne? Kundin tsarin mulkin kasar nan ya bai wa kowane dan Najeriya damar ya tsaya takarar shugabancin karamar hukuma, ko jiha ko kasa sai biyu. Don haka bai kamata wani ya fito ya ce zai hana wani tsayawa takarar ba. Wannan ba dimokuradiyya ba ce, idan muka ce haka mun kauce daga tsarin mulkin dimokuradiyya. Don haka idan Shugaban Buhari ya ga cewa yana da abubuwan da yake son ya yi wa ’yan Najeriya, a bar shi ya sake fitowa takara. Ba shi kadai ne zai tsaya takara ba, akwai wasu jam’iyyu da dama da za su tsayar da ’yan takararsu, a bar jama’a su zabi wanda suke ganin cewa ya dace kuma ya cancanta.

Yaya kake kallon rikicin Fulani makiyaya da manoma da suke faruwa a kasar nan?

 Bai kamata a rika samun rikice-rikice a tsakanin Fulani makiyaya da manoma ba, domin manoma suna noma shinkafa da dawa da masara da sauran kayan amfanin gona da muke ci. Haka Fulani makiyaya da suke kiwon shanu da awaki da tumaki suna samar mana da nama da madara da taki. Ka ga dukan wadannan bangarori ana amfana da juna, don haka kamata yi a ci gaba da tafiya tare, kamar yadda aka saba, ba a tsaya ana rikice-rikice ba. Dukan wadannan bangarori manoma da makiyaya arziki ne kowanensu yake samarwa, idan muka hada wadannan bangarori za a ga arzikin kasar nan ya karu.

Yanzu Najeriya mun dogara da man fetur ne, amma man nan kullum farashinsa sauka yake yi a kasuwar duniya. Don haka akwai lokacin da zai zo da ba za a samu kudin man nan ba. A Najeriya muna da filayen noma da kiwo ya kamata mu hada karfi kowa ya tashi, manoma su ci gaba da bunkasa noma, makiyaya su ci gaba da bunkasa kiwon da suke yi, idan muka yi haka sai kasar nan ta bunkasa. Don haka bai kamata mu tsaya muna rikice-rikice ba.

Wane sako ne  kake da shi zuwa ga shugabannin Najeriya?

Shugabannin Najeriya su rika fita kauyuka domin su ga yadda da jama’a suke ciki. Misali kamar ’yan Majalisar Dokoki ta kasa wato sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai bai kamata su rika zama a Abuja daga ranakun Litinin zuwa Juma’a ba. Ya kamata su rika daukar lokaci suna zuwa mazabunsu a kauyuka suna ganin halin da mutanensu suke ciki. 

Haka gwamnoni da ministoci aikinsu ba a Abuja kadai yake ba, a kullum za ka ji cewa Gwamna ba ya gida ya bar jiharsa ya tafi Abuja. Haka gwamnoni suke yi daga kowane bangare na kasar nan. Gaskiya suna barin talakawansu da wahala da yunwa, don haka yana da kyau su canja halayensu su rika zama cikin jama’arsu. 

 Shi ma Shugaban kasa ya kamata ya rika samun lokaci yana kai ziyara kauyuka yana ganin halin da al’umma suke ciki. Bai kamata ya rika tsayawa a cikin birane kadai ba, ya rika zuwa kauyuka inda wahala da rashin hanyoyi da rashin ruwa da rashin makarantu da rashin asibitoci suke, haka ya kamata shugabannin Najeriya su rika yi. 

Amma sai dai ka ji cewa kullum sun tafi Abuja ko kasashen waje, za ka ji shugabannin Najeriya suna tafiya Dubai ko wata kasar Turai, don sayo kayayyakin bikin Kirsimeti ko bikin Sallah. Dukiyar Najeriya ba ta shugabanni ce kadai ba, talakawa da matasa da mata da ba su da cin yau balle na gobe suna da hakki, don haka shugabanni su rika kulawa suna tallafa wa irin wadannan mutane.