✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fadar Buhari ta mayar wa da Bishop Kukah martani

Fadar Shugaban Kasa ta ce, kalaman Bishop Kukah ba su dace da malamin addini ba

Fadar Shugaban Kasa ta zargi Bishop Mathew Hassan Kukah da cusa siyasa a sha’anin addini, inda ta ce lafuzan da ya yi kan Shugaba Buhari ba su dace su fito daga bakin malamin addini ba.

A hudubarsa ta bikin Easter da ya gabatar ranar Lahadi, Bishop Kukah wanda shi ne shugaban Kiristocin darikar Katolika a yankin Sakkwato, ya bayyana damuwa kan halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki na tabarbarewar tsaro.

Ya kuma soki Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya ce nauyin tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar ya rataya a wuyanta.

A cikin hudubar mai taken “Najeriya: Gabanin gushewar daukakarmu”, Bishop Kukah ya ce Najeriya ta zamto tamkar wani dandalin kisa, ganin yadda mayakan Boko Haram da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka.

Sai dai a yayin mayar da martani, mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce kalaman Bishop Kukah sun saba da na masanin addini.

Ya ce, “Duk ’yan kasa suna da akidunsu na daban, hatta nau’ukansu na fadin gaskiya sun bambanta, amma idan ka ce kai bawan Allah ne, kamar yadda Bishop Kukah yake yi, ya kamata akidarsa ta tsaya a kan hanyar gaskiya da adalci.

“Bishop Kukah ya fadi wasu abubuwa wadanda ba za a iya fassarawa ba a yayin wa’azin da ya yi na Ista.

“Amma, da yake cewa ta’addancin Boko Haram ya fi wanda aka yi a 2015 muni, bai yi magana kamar bawan Allah ba.

“Bishop Kukah ya kamata ya je Borno ko Adamawa don tambayar al’ummar bambanci tsakanin 2014 da 2021.

“Yana taka rawar siyasar bangaranci inda yake jan Shugaban Kasa cikin lamarin.

“Gwamnatin da ta kirkiro wata ma’aikata mai zaman kanta karon farko a tarihin kasar, don magance matsalolin ’yan gudun hijira, ya za a yi a zarge ta da gazawar kula da su,” a cewar Garba Shehu.