Fadan cikin gida a tsakanin wasu ’yan bindiga daga yankin Batsari na Jihar Katsina da abokan hamayyarsu daga Jihar Zamfara ya dada kamari.
Wata majiya ta tabbatar da cewa ’yan bindigar na yankin Batsari suna afka wa duk bakon barawon da suka gani ya fito daga yankin Zamfara, ko kuma yaran Dangote, wanda ke da iyaka da Jibiya da kuma Zamfara.
- Ma’aikatan asibiti 3 sun shiga hannu kan satar jarirai
- Majalisa ta ba da umarnin bincike kan kisan Kwamishinan Katsina
Majiyar ta ce, yankunan Nahuta da Madogara da Zamfarawa da Tashar Modibbo da wasu kananan garuruwa, duk na karkashin ikon dan bindigar nan, Abu Radda.
Ya umurci yaransa su kama duk wani bakon barawo da suka gani a yankunan.
Kazalika, shi ma dan bindigar nan mai suna Abdu Mai Komi, na da yankunan da yake iko da su kamar su Gobirawa, Garin Runji, Garin Yara, Kondatso da kuma Yasure.
Shi ma ya hada kai da Abu Radda a kan kai hari ga duk wani dan bindigar da suka gani a yankin.
Rahotanni sun ce hare-haren da aka kai yankin Batagarawa na Jihar Katsina, yaran nasu ne suka kai shi.
Amma bayan maharan sun gama ta’addacinsu a garin Batagarawa a hanyarsu ta komawa sansanin Dangote da ke dajin Shimfida, yaran Abu Radda da na Abdu Mai Komai suka yi musu kwanton-bauna suka kwace duk dabbobin da suka sato, tare da kashe wasu daga cikinsu, wasu kuma suka tsere.
Bayanai sun nuna cewar mazauna kauyukan da ke yankin Ruma Tsohuwa, sun ga yadda aka tafka gumurzun.
Majiyar, ta ce bayan sun kwace dabbobin da makaman da suka kwace shanun, sun raba a tsakaninsu da wasu barayin da suka taimaka musu.
Rahotanni dai sun ce lamarin ya yi kamarin da har wasu daga cikin manyan yaran Dangote suka yi kaura daga sansaninsu suka koma cikin wani dajin.
Har wa yau, fadan ya jawo dukkan bangarorin biyun ba wanda ya ke yawo da makami saboda kar a farmake shi.
Kazalika, an ce ’yan bindigar yankin Batsari na son samun cikakken iko ba tare sa kutse da wasu ke musu daga Jihar Zamfara ba.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isa, ya ce zai bincika tare da gano lamarin da ke faruwar, bayan tuntubarsa da aka yi.