An dawo musayar wuta ba kakkautawa a Khartoum, babban birnin kasar Sudan a ranar Laraba ’yan mintuna bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar.
Kasashen Amurka d Saudiyya ne dai suka jagoranci sasancin wanda ya kare da sanyin safiyar Laraba.
- A mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara da aka tsige kujerarsa – Kotu
- YANZU-YANZU: Abba Kabir ya mayar da Muhuyi Magaji kujerarsa
Tun da yammacin Talata ne aka fara jiyo karar harbe-harbe a hedkwatar hukumar leken asirin kasar, inda kowanne bangaren rikicin ke zargin abokin fafatawarsa da karya yarjejeniyar ta awa 72.
Wata majiya a rundunar sojin kasar, wacce Abdel Fattah al-Burhan, ke jagoranta, ta zargi kungiyoyin RSF wadanda ke karkashin Mohamed Hamdan Daglo da kai hare-hare a kan ginin.
Ita ma wata majiya a RSF, ta ce, “wani jirgin sojoji mara matuki ya jefa bama-bamai a kan ginin da dakarun RSF suka yi sansani, inda suka rika ruwa wuta sannan suka lalata wani bangaren ginin hedkwatar hukumar leken asirin kasar.
Da sanyin safiyar Laraba, mazauna garin Omburman, wanda ke dab da kogin Nile a kusa da birnin Khartoum, sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe ’yan mintuna bayan yarjejeniyar ta kare da misalin karfe 6:00 na safe, a agogon kasar.
Tun bayan fara fadan a ranar 15 ga watan Afrilu, sama da mutum 2,000 ne aka kashe a rikicin siyasar tsakanin rundunonin biyu
Kazalika, sama da mutum miliyan biyu da rabi ne suka bar muhallansu, inda daga ciki sama da mutum 550,000 suka nemi mafaka a makwabtan kasashe, kamar yadda Hukumar da ke Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.