Jama’a suna ta tserewa bayan barkewar musayar tsakanin sojoji da ’yan banga a yankin Ndele da ke Karamar Emuoha ta Jihar Ribas.
Rikicin ya barke ne bayan wata cacar baka tsakanin sojojin da ke gadin wanin kamfani mai da mambobin haramtacciyar kungiyar ’yan banga, har lamarin ya kai ga musayar wuta.
’Yan bangar, karkashin wani mai sun a Gift, sun harbi biyu daga cikin sojojin, suka daure su, suka kwashe kakinsu da bindigoginsu, sannan suka arce zuwa cikin daji.
- Babu lallai a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Alhamis —Masana
- Dan shekara 29 ya doke dan Majalisar Tarayya mai ci a Imo
Hakan ya sa aka turo karin sojoji, domin cafke bata-garin da kuma kwato bindigogi da kakin sojojin da suka harba.
Sojojin sun ritsa Gift a maboyarsa, inda bangarorin biyu suka yi musayar wuta, sai dai babu labarin ko an samu rauni ko asarar rai a garin hakan.
Gift ya samu ya tsere amma sojojin sun je gidansa suka cinna masa wuta, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba suka yi ya ta kaura saboda gudun kar harsashi ya same su.
Basaraken yankin, Damian Ejiowhor, ya ce tun yammacin ranar Asabar sojoji ke yankin suna neman Gift da bindigogin da ya dauke.
Wakilinmu ya yi kokarin ji daga bakin kakakin Runduna ta 6 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Fatakwal, Iweha Ikedichi, amma bai amsa kiran wakilin namu ba, kuma bai amsa rubutaccen sakon da aka aika masa ba, har aka kammala hada wannan rahoto.