Fada ya barke a tsakanin kabilun Hausawa da Nuba a Kosti, babban birnin Jihar White Nile da ke Kudancin Sudan, wato yankin da ke da iyaka da Sudan ta Kudu.
Ana dai kallon tashin hankalin ba shi da alaka da manyan fadace-fadacen soji da suka barke a fadin kasar Sudan tun ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin dakarun da ke biyayya ga janar-janar guda biyu wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 750.
- Majalisar Sakkwato ta kafa dokar hana tsadar aure
- ’Yan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sakkwato
An dade ana zaman dar dar a tsakanin kabilun da ake ganin hakan ya ta’allaka ne kan takaddamar ruwan sha da albarkatun kasa tsakanin manoma da makiyaya wanda kuma galibi yakan tayar da hankalin al’ummomin bangarorin biyu.
Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya janyo rikicin baya-bayan nan a White Nile ba, wanda rahoton ya ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane 16 daga bangarorin biyu, tare da raunata adadi mai yawa, da kona wasu gidaje.
Rikicin da ya barke a watan Oktoba a Jihar Blue Nile mai makwabtaka da kasar, ya samo asali ne tsakanin Hausawa da wasu kungiyoyi tare da kashe akalla mutane 200 cikin kwanaki biyu.
Hausawa ’yan asalin kasar Sudan, wani bangare ne na wata babbar kabila ta Afirka, wadanda ke zargin cewa ana nuna musu wariya ta hanyar daukarsu a matsayin bare da kuma hana su mallakar filaye a Blue Nile.
Tsakanin watan Yuli zuwa farkon Oktoban bara, an kashe akalla mutane 149, yayin da wasu 65,000 suka rasa matsugunansu a Blue Nile, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Samun filayen noma yakan haifar da tashe-tashen hankula a kasar da ke fama da talauci, inda noma da kiwo ke da kashi 43 cikin 100 na ayyukan yi da kuma sama da kashi 30 na ma’aunin GDP a cewar bayanan Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya.
Kasar Sudan dai ta fada cikin rudani tun bayan da rikicin mulki ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya ga Babban Hafsan Soji, Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta Rapid Support Forces.
Ya zuwa yanzu dai fadan da aka gwabza a Khartoum babban birnin kasar da wasu garuruwa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 750 tare da raunata dubban mutane da kuma raba dubunnai da muhallansu, yayin da ’yan gudun hijira da dama suka tsere daga kasar.
RFI