✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Da jarin N100 wani yaro ya yi shagon kansa a kwana 10

Ya fara da kasa kayan N100 a cikin kwali, amma cikin kwana 10 har ya yi shagon kansa

Wani karamin yaro da ya fara kasuwanci kamar wasa a cikin dan kwali da kayan da ba su kai Naira 100 ya zama cikakken dan tireda a kwana 10.

Kimanin mako biyu da suka gabata ne kafafen sada zumunta suka cika da hotunan wani yaro da ke zaune a wani dan shagonsa na kwali da ya bude, inda ya zuba kayan tireda na Naira 100 a cikin kwalin da nufin sayarwa a garin Rano da ke Jihar Kano.

Hakan ya jawo wa yaron mai suna Isma’il daukaka, inda bayan an yi ta yada hotunansa, aka rika samun wadansu suna kai masa tallafi.

Hakan ya sa hatta shagon ya canja rayuwar mahaifinsa kamar yadda ya shaida wa Aminiya.

Shagon Isma’il ya canja min rayuwa Mahaifinsa

Malam Yusuf Muhammad shi ne mahaifin Isma’il wanda ake yi wa lakabi da Sabon Dan Kasuwa a garin Rano da ke Jihar Kano da ya

fara kasuwanci a cikin kwali kafin daga bisani ya samu babban shago da aka bude masa da taimakon jama’a.

Ya shaida wa Aminiya cewa bude shagon da aka yi wa dansa ya sauya rayuwarsa gaba daya, inda a yanzu yake samun budin kula da iyalinsa.

Malam Yusuf wanda tsohon ma’aikacin gidan mai na A. A RANO ne ya ce tun daga lokacin da aka yi masa ritaya daga aiki a bara, ya zama ba abin da yake yi sai dan noma sai yanzu da Allah Ya kawo wa dansa budi ta wannan hanya.

“Kasancewar a yanz ba ni da aikin yi, ni nake zama a shagon tare da Isma’il ina kula da shi da kasuwancin nasa.

Kin san har yanzu yaro ne, don haka ni nake kula da shagon tare

da shi,” inji shi.

Da yake bayyana wa Aminiya tarihin shigar dansa kasuwancin, Malam Yusuf ya ce dama Isma’il yana da zuciyar neman na kansa domin ainihin kudin da ya fara sayar da kayan masarufin ya samo su ne daga aikin leburanci da ya yi.

“Aikin kwashe kwatami suka yi wa wani mutum mai suna Dahiru shi

ne ya ba su ladan Naira 400, abokin aikinsa ya dauki Naira 300 shi kuma aka ba shi Naira 100.

“A nan ne ya dauki wannan kudi ya sayo magi da ashana da sauransu, inda ya samu kwali ya zuba a ciki ya samu benci a kofar gida ya zauna yana tallar kayansa.

“A nan ne wata makwabciyarmu ta zo wucewa ya yi mata tallar magi har ta yi masa ba’a cewa ba za ta saya ba.

“Sai wani makwabcinmu da ya ji abin da matar ta yi masa sai ya zo ya sayi magin Naira 55.

“To daga nan ne sai Isma’ila ya je ya sake sayo wani magin da wannan kudi ya sake kasawa.

“Ganin haka ya sa shi wancan mutum ya dauki hotonsa ya dora a kafar sadar zumunta ta Facebook inda kuma daga nan ne jama’a suka yi ta magana har aka karbi lambar wayata da asusuna na banki inda jama’a suka tallafa masa da kimanin Naira dubu 100 don ya bunkasa shagon nasa.

“A wannan lokaci ma wani mutum daga Kaduna ya kawo masa katan 10 na kayayyakin masarufi tare da rabin buhun gishiri da na sukari.

“To da wannan kudi da kayayyaki da aka samu aka bude masa babban shagon nan,” inji shi.

Wadansu sun ce za su dauki karatunsa zuwa jami’a

Mahaifin Isma’il Sabon Dan Kasuwa ya ce kasuwancin dansa ba zai hana shi gudanar da karatunsa ba.

“Yarona a yanzu yana makarantar firamare, wannan harka ta kasuwanci da ya shiga ba za ta hana shi karatunsa ba.

“A yanzu ma don ana hutun cutar korona ne ya sa yake zaune yake kasuwanci, amma da zarar an koma makaranata zai koma karatunsa.

“A yanzu haka akwai wani bababn mutum daga Jigawa ya ce zai dauki nauyin karatunsa.

“A yanzu ma ya nemi yardarmu cewa za kai shi Makarantar Model da ke Dutse a Jihar Jigawa. Wani ma a Jihar Katsina ya yi wannan alkawari na daukar nauyin karatunsa har jami’a.

“To dai a yanzu muna nan muna addu’a Allah Ya zaba mana abin da ya fi alheri”, inji shi.

Malam Yusuf ya mika godiyarsa ga jama’a musamman wadanda suka yi wa dansa wannan tagomashi.

Dama ina da sha’awar kasuwanci Isma’il

A tattaunawar Aminiya da yaro Isma’il Yusuf dan kimanin shekara 11, ya ce shi dama yana sha’awar kasuwanci don haka zai ci gaba da wannan harka har girmansa.

Isma’il Sabon Dan Kasuwa ya ce duk da cewa yana karatu a halin yanzu amma hakan ba zai shafi sha’anin kasuwancinsa ba.

“Idan na koma makaranata zan ci gaba da karatuna haka kuma kasuwancin ma ba dainawa zan yi ba.

“Sai dai mahaifina ne zai ci gaba da kula min da dukiyata”, inji shi.

Aminiya ta lura da yadda wannan abu ya zama abin kwaikwayo ganin yadda mutane daban-daban suke kwaikwayon Isma’il inda suke sanya hotunasu a shafukan sada zumunta musamman na Facebook wanda ke nuna yadda suka kasa kayayayain masarufi a cikin kwalaye.

Abin da ya sa tallafa wa Isma’ila –Malam Ibrahim Yala

Bayan yada hotunan Isma’il da aka yi a Facebook, wani fitaccen dan siyasa daga Jihar Kaduna, wanda ya yi fitacciyar wakar nan ta ‘Yau Najeriya Riko Sai Mai Gaskiya’, Malam Ibrahim Yala ya bayyana wa Aminiya cewa ya tallafa wa Ismai’l ne saboda ya kara karfafa shi wajen neman na kansa.

“Abin da ya ja hankalina ga wannan yaron yana tuna min rayuwata lokacin da nake yaro.

“Domin iyayena da na kusa da ni za su shaida hakan cewa ni mutum ne

mai kokarin neman na kaina. Da kaina ma nake kera dan akwakun da nake zuba kayan masarufi a ciki in sayar.

“Kuma idan lokacin rake ne nakan sayo rake in yanka in kasa in sayar a kofar gida.

“Don haka na ga dama ce a gare ni da zan tallafa masa don shi ma nan gaba idan ya girma ya tallafa wa wadansu.

“Ganin cewa akwai masu tallafawa da kudi sai na zabi in sayo kayan shago don haka na sayi kayayyakin masarufi na kai masa daga nan Jihar Kaduna har zuwa can Rano”, inji shi.