✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Facebook ya bi sahun Twitter wajen goge sakon Buhari

Ya ce ya goge sakon da Buhari ya wallafa ne saboda ya karya ka’idojinsa.

Shafin Facebook ya bayyana goge wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa kan abin da ya kira ‘saba’ ka’idojin zauren na tayar da zaune tsaye.

Facebook ya ce sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa karan tsaye ne ga ka’idojinsa, don haka ya goge sakon bayan korafin da wadansu ’yan Najeriya suka yi ta aika wa shafin. 

A ranar Talata ce Shugaba Buhari ya yi barazanar maganin ’yan awaren IPOB da ke faman kai hare-hare kan wasu Hukumomin Gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

A cikin sako nasa, Buhari ya ce zai yi maganin masu tayar da kayar bayan kamar yadda sojojin Najeriya suka yi wa ’yan tawaye a lokacin yakin basasa, wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka fafata a yakin da ya ci rayukan fiye da mutum miliyan guda.

“Galibin masu ta da kayar baya a yanzu suna da karancin shekaru da za su iya fahimtar girman barnar da irin hasarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a lokacin yakin basasa ba. 

“Mu da muka shafe tsawon shekara talatin muka fafata a fagen fama, mun san bala’in yakin, kuma za mu yi maganin su da yaren da suka fi fahimta,” a cewar Buhari cikin sakon da ya wallafa a shafin.

Sakon da shugaban ya wallafa wanda wadansu mutane suka fassara da barazanar ‘kisan kiyashi’, shafin Twitter ne ya fara goge shi daga kan kafar sada zumuntar a ranar  Laraba.

Shi ma shafin Twitter ya ce ya goge sakon da Buhari ya wallafa ne saboda ya karya ka’idojinsa.