Shafin Facebook ya bayyana goge wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa kan abin da ya kira ‘saba’ ka’idojin zauren na tayar da zaune tsaye.
Facebook ya ce sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa karan tsaye ne ga ka’idojinsa, don haka ya goge sakon bayan korafin da wadansu ’yan Najeriya suka yi ta aika wa shafin.
- Gwamnati ta dakatar da ayyukan shafin Twitter a Najeriya
- Najeriya na zargin Twitter da hannu a fafutikar kafa kasar Biyafara
A ranar Talata ce Shugaba Buhari ya yi barazanar maganin ’yan awaren IPOB da ke faman kai hare-hare kan wasu Hukumomin Gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
A cikin sako nasa, Buhari ya ce zai yi maganin masu tayar da kayar bayan kamar yadda sojojin Najeriya suka yi wa ’yan tawaye a lokacin yakin basasa, wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka fafata a yakin da ya ci rayukan fiye da mutum miliyan guda.
“Galibin masu ta da kayar baya a yanzu suna da karancin shekaru da za su iya fahimtar girman barnar da irin hasarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a lokacin yakin basasa ba.
“Mu da muka shafe tsawon shekara talatin muka fafata a fagen fama, mun san bala’in yakin, kuma za mu yi maganin su da yaren da suka fi fahimta,” a cewar Buhari cikin sakon da ya wallafa a shafin.
Sakon da shugaban ya wallafa wanda wadansu mutane suka fassara da barazanar ‘kisan kiyashi’, shafin Twitter ne ya fara goge shi daga kan kafar sada zumuntar a ranar Laraba.
Shi ma shafin Twitter ya ce ya goge sakon da Buhari ya wallafa ne saboda ya karya ka’idojinsa.