✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fabregas ya zama sabon kociyan kungiyar Como ta Italiya

Ya buga wa kungiyar wasa 17 a bara, wadda take Serie B.

An nada tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea da Barcelona Cesc Fabregas kociyan Como ta Italiya a matakin rikon kwarya.

Fabregas, mai shekara 36, wanda zai fara aikin horar da tamaula a karonsa na farko, zai maye gurbin Moreno Longo.

Ya buga wa kungiyar wasa 17 a bara, wadda take Serie B, daga nan ya yi ritaya daga taka leda ya zama kociyan karamar kungiyar.

Wasan farko da Fabregas zai ja ragama shi ne wanda za su karbi bakunci Feralpisalo ranar 25 ga watan Nuwamba, bayan an kammala wasa na kasa da kasa.

Como tana ta shida a kan teburi da maki 21, bayan buga karawa 12 a kakar nan.

Fabregas ya koma Como a Agustan 2022 bayan da ya bar Monaco, ya kuma zuba hannun jari a kungiyar ta Italiya tare da abokinsa, Thierry Henry.

Tsohon dan wasan tawagar Ingila da Chelsea, Dennis Wise shi ne shugaban kungiyar, wanda ya koma can a Mayun 2019.