✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kananan yara masu gararamba ke karuwa a titunan Kano

Akwai takaici yadda yaran suke koyon halaye marasa kyau tun suna kanana.

Mazauna cikin kwaryar Kano sun bayyana damuwarsu game da yawaitar yara kananan da ke gararamba a kan tituna kuma wadanda ba su da gidajen kwana inda jama’a da dama ke ganin hakan a matsayin barazana ga zaman lafiyar jihar da ke da tarihin zaman lafiya.

Ana ganin yawaitar irin wadannan yaran da shekarunsu bai wuce na zuwa makaranta ba amma suka buge da yawo a kan tituna da rana kuma suke kwana a gefen tituna da shaguna da daddare baban barazana ce ga harkar tsaro a garin.

Yaran, an ce sun fi yawaita a yankin Sabon Gari ne da ke Karamar Hukumar Fagge, sai kuma yankin Titin gidan Zoo da Tashar Jirgin Kasa da Titin Bello da sauran wurare.

Babban abin takaici ne ganin irin wadannan yara da suke samun abin sakawa a bakin salati ta hanyar baracebarace da kuma abin da wasu masu tausaya musu ke ba su, kamar yadda bincike Aminiya ya tabbatar.

Har ila yau, binciken wannan jarida ya tabbatar da mafiya yawan irin wadannan yaran ba ‘yan asalin jihar Kano ba ne sai dai suna shigowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da jihar da suka hada da Katsina da Yobe da Borno da Zamfara da wasu sassan jihar Kaduna.

Wasunsu su kan biyo sa’anni ne yayinda wasu kuma almajirai ne da ba su samu cikakkiyar kulawa da sa ido ba.

Wani yaro dan shekara 13 mai suna Abba Bala da ke kwana a kan titi ya shaida wa Aminiya cewa shi dan asalin garin Kamuya Wuru ne daga jihar Yobe.

Ya ce hare-haren ta’addanci ne a jihar Yobe ya raba shi da garinsu bayan rasa mahaifinsa inda wani ya kawo shi Jihar Kano da sunan zai kai shi wajen mahaifiyarsa da take ‘yar asalin jihar Adamawa amma mazauniyar Jihar Kaduna.

“Ni ban ga mahaifiyata ba tsawon lokaci. Lokacin da muke zuwa nan an dora ni ne a kan babbar mota zuwa Kwanar Dawaki daga nan muka shigo cikin Kano.

“Bayan wasu ‘yan kwanaki sai shi wanda ya kawo ni ya gudu ya bar ni ni kadai kuma ni ban san kowa ba sannan ba ni da kudin da zan iya komawa.

“Ina kwana a dandamalin shago ne, ba ni da abin da zan ci, wasu lokuta ma nakan samu abin da zan ci ne kawai daga abin da wasu suka ci suka rage,” inji shi.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana shaye-shaye sai yace yana shan taba sigari ne kawai banda na kwayoyi, “Ni ba na shaye-shayen kwayoyi.

“Sigarin ma na fara sha ne da aka ce min zai rika rage min damuwa da saukaka min jin yunwa,” inji shi.

Shi ma wani dan shekara 14 da ke garabamba a Kano mai suna Muhammad Abdullahi ya ce yana kwana ne a titunan Sabon Gari, amma shi dan asalin Jihar Adamawa ne.

Ya ce ya zo Kano ne domin neman kudi, amma kuma sai ya samu akasin haka. “Na yi zaton akwai ayyukan yi da yawa a Kano da zan rika samun kudi, amma da na zo sai na ga ashe ba haka lamarin yake ba.

“Yanzu a titi nake kwana ko barandan shaguna, wasu lokutan kuma nakan samu Masallaci in kwanta. Nakan yi bola-bola domin samun na kashewa.”

Da aka tambaye shi ko yana shayeshaye, sai ya ce, “Gaskiya ina shayeshayen kwayoyi, amma ina ta kokarin dainawa na kasa,” inji shi.

Shi ma mai suna Umar Abdullahi mai shekara 12 da Aminiya ta tsinta a titin Zoo tare da wasu abokansa suna bola-bola, ya ce daga Batsarin Jihar Katsina ya fito bayan ’yan bindiga sun kashe iyayensa.

Ya kara da cewa ya samu tserewa daga garinsu ne domin firgici, sannan ya yanke shawarar zuwa Kano domin cigaba da rayuwa, amma rayuwar sai a hankali kasancewar a titi yake rayuwa.

“Ban san kowa a Kano ba, sannan yanzu ban san inda ’yan uwana suke a Katsina ba. Yanzu ’yan uwana da na sani kawai su ne wadannan abokan nawa da muke yawo tare muna bola-bola, sannan idan dare ya yi mu nemi waje mu kwanta.

“Sai dare ya raba muke neman barandar shago a titin Zoo mu kwanta, sannan muna tashi da sauri kafin gari ya waye, mu kara gaba.

“Yawancinmu ba mu da muke yawo tare ba mu san kowa a Kano ba, amma muna cigaba da rayuwa,” inji Abdullahi.

Mis Mary Joseph, wata ’yar kasuwa ce a Sabon Gari, ta bayyana wa Aminiya cewa ko kadan ba ta jin dadin ganin kananan yara suna garabamba a titi, musamman ma yadda suke kwana a titi.

Ta kara da cewa duk da cewa yaran abin tausayi ne, amma ya zama dole a rika jin tsoron mu’amala da su kasancewar yanayin rayuwa ya canja sosai yanzu.

“Nakan yi mamaki tare da tunanin wai ina iyayen wadannan kananan yaran suke?”

Wani mazaunin Sabon Gari, Mista Bitrus Bitrus ya bayyana wa Aminiya ba ya ganin laifin kowa sai na iyayen yaran da suka gaza daukar dawainiyar yaransu, da kuma gwamnatin jihar bisa gazawarta na tilasta wa iyayen su yi abin da ya dace.

“Dalilin da ya san a ce akwai laifin gwamnati shi ne tana da karfin ikon tattara yaran, ta tambaye su daga inda suka fito, sannan ta kwashe su ta mayar da su wajen iyayensu, sannan a tilasta iyayen daukar dawainiyarsu.

“Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta taimaka wajen kwashe yaran nan a mayar da su garuruwansu wajen iyayensu ko ’yan uwansu saboda halayen da yaran suke nuna akwai ban tsoro,” inji shi.

Usman Eder wani mai shago ne a titin Zoo da ke Kano, ya ce babbar matsalar ma ita ce yadda yaran suke mu’amala da manyan masu garabamba irin su.

Ya kara da cewa yawanci tare suke rayuwa, tare suke kwana, kuma a cewar shi yawancin manyan masu garabamban, masu laifi ne, wasu ma sun sha zuwa gidan yari.

“Na samu labarin cewa an shigar da wasu yara masu garabamban wasu kungiyar barayi ta Arobaga a Sabon Gari, inda suke tafiya sace-sacensu a gungun mutum biyar zuwa 20 dauke da makamai,” inji shi.

A nasa bangaren, kwamandan ’yan bangan Sabon Gari, Suraj Ali ya ce daga cikin manyan kalubalen da suke fuskanta akwai fama da wadannan yaran masu garabamba a titunan Kano, sai dai ya ce a bangarensu suna kokari, sannan suna ta kokarin hada gwiwa da Rundunar ’Yan sandan jihar domin tsara hanyoyin da za bi a magance matsalar cikin sauki.

“Akwai takaici yadda yaran suke koyon halaye marasa kyau tun suna kanana, saboda idan har dan karamin yaro mai shekara 13 zai iya dauka wuka ya cutar da mutane idan zai musu kwace ko sata, to ai ka ga lallai akwai matsala.

“Mu a matsayinmu na masu bayar da tsaro muna ta kokarinmu wajen magance matsalar nan, musamman a Sabon Gari,” inji shi.