Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma Liverpool za su barje gumi a wasan karshe na Gasar Kofin FA na Ingila.
Za a buga wasan da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar Asabar a filin wasa na Wembley da ke Landan.
- Kar a yadda a shiga kakar zabe jami’o’i na rufe – Farfesa Alkali
- 2023: Can ta matse wa ’yan Najeriya, dadina nake ji —Emefiele
Chelsea za ta kara wasan na karshe ne ba tare da ’yan wasanta; Mattio Kovacic, Ben ChilWell da kuma Hudson-Odoi ba, sakamakon rauni da suke fama da shi.
Liverpool kuwa za ta buga wasan ne ba tare da dan wasan tsakiyarta ba Fabinho ba.
Ana sa ran ’yan kallo mutum 90,000 ne za su shiga filin don kallon wasan karshen na Gasar FA.
Ana hasashen Liverpool na iya lashe gasar, ganin yadda take nuna bajinta a bana.
A baya-bayan nan Liverpool ta lashe Kofin Carabao, inda ta lallasa Manchester City da ci 3 da 2 a wasan karshe.
Har wa yau Liverpool na mataki na biyu a Gasar Firimiyar Ingila, inda Manchester City ta ba ta tazarar maki uku.
Ita kuwa Chelsea tana mataki na uku a Gasar Firimiyar Ingila da maki 70, lamarin da sanya ba ta cikin jerin kungiyoyin da za su iya lashe gasar.
Ana sa ran wasan zai kayatar, inda ake tunanin ’yan wasa kamar su Mohamed Salah, Sadio Mane, Luis Diaz da Farmino daga Liverpool za su baje kolinsu.
Chelsea na da taurarin ’yan wasa irin su; Pulisic, Mason Mount, Lukaku, Kai Harvertz da Timo Werner, wadanda za su taka wa mata rawa.