✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Europa: An kai wa magoya bayan Man U hari a Poland

An kai wa magoya bayan kulob din hari a jajibirin wasan karshen gasar Europa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce magoya bayanta aka nufa da harin ranar Talata da dare a wata mashaya a birnin Gdansk na kasa Poland gabanin wasan karshe na kofin Europa.

A ranar ranar Laraba da dare za buga wasan karshe na gasar cin kofin Europa tsakanin Manchester United Villareal a birnin Gdansk na Poland.

Wani bidiyo ya nuna gungun wadansu mutane galibinsu sanye da bakaken kaya na tserewa daga wata mashaya a birnin Gdansk, inda suka bar kujeru da tebura a wargaje.

Wani bidiyon na daban ya nuna wajen da yammaci inda magoya bayan Man U din suke rera wakoki a wasan farko da suka samu damar da za a kara a wajen tun bara sakamakon annobar COVID-19.

Sanarwar da Manchester United ta ta fitar ta ce: “Ma’aikatan kulob din na tallafa wa wadansu magoya bayanmu tun jiya (Talata) zuwa yau (Laraba) a Gdansk inda aka kai musu hari a wata mashaya.”

An ce magoya baya uku ne suka samu raunuka.

An ware wa magoya bayan Manchester United tikiti dubu biyu kacal inda kusan rabinsu sai a ranar Laraba ne za su shiga birnin na Gdansk.

Shugaban Gdansk, Aleksandra Dulkiewicz, ya yi tofin Allah tsine kan harin da aka kai.

Ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa, “Duk wani nau’in tayar da zaune tsaye ba zai samu gindin zama ba a nan,” sannan yana maraba da magoya bayan Man U.