✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EURO: Ingila ta sha da ƙyar a hannun Slovakia

Jude Bellingham da Harry Kane sun kai Ingila zagaye na gaba na Gasar Euro.

Ƙasar Ingila ta sha ƙyar a hannun Slovakia bayan ta yi nasara da ci 2-1 a wasan zagaye na 16 na Gasar Euro da ake bugawa a ƙasar Jamus.

Ɗan wasan gaban Slovakia, Ivan Schranz ne, ya fara jefa ƙwallo a minti na 25 da fara wasan.

Ingila ta warware ƙwallon ta hannun ɗan wasan gabanta, Phil Foden, amma na’urar VAR ta kashe ƙwallon sakamakon satar fage da ɗan wasan ya yi.

Ingila ta mamaye filin inda ta dinga kai hare-hare, sai a minti na 95 ta samu damar warware ƙwallon ta hannun ɗan wasan gabanta, Jude Bellingham.

An tashi wasan da ci 1-1, inda aka tafi hutun ƙarin lokaci na minti 15, wanda a nan ne Harry Kane ya sake jefa wa Ingila ƙwallo ta biyu a raga.

Da haka ne aka ƙarƙare wasan, inda Ingila ta mamaye ko ina na filin.

Bayan tashi daga wasan an bai wa Jude Bellingham kyautar gwarzon ɗan wasan da ya fi hazaƙa a wasan.