Kungiyar Tarayyar Turai ta fara shirin haramta sayen danyen mai daga Rasha, a matsayin wani bangare na karin takunkumin da take kakaba wa Rasha sakamakon mamayar Ukraine da ta yi.
Kungiyar Tarayyar Turan, wadda ita ke da alhakin tsara takunkumi, ta shirya wani daftari da zai isa ga mambabin kungiyar 27 a ranar Laraba don daukar mataki kan Rasha.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Ke Hana Mata Zuwa Masallacin Idi
- Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar bene mai hawa 3 a Legas
Jami’an diflomasiya da dama sun ce wannan mataki na Tarayyyar Turai mai yiwuwa ne, sakamakon canza shawarar da Jamus ta yi, bayan da tun da farko ta nuna rashin amincewa da haramta sayen danyen man Rasha, inda ta ce matakin zai raunana tattalin arzikin Rashan.
Jagoran manufofin hulda da kasashen wajen na Tarayyar Turai, Josep Borrell, ya ce Rasha na zafafa hare-hare a kan Ukraine, lamarin da ya sa karin sabbin takunkumai a kanta ya zama wajibi.
Hukumar za ta gabatar da shirin haramta sayen man Rasha da zai fara aiki nan da wata shida ko bakwai mai zuwa, don bai wa kasashen Turai damar kintsawa wajen fadada hanyoyin samun makamashinsu.