Shugaban Kungiyar Malaman Jami’oin (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi, ya koka cewar kasar Ethiopia da Jami’oin kudi sun fara kwashe musu farfesoshi da malamai saboda gazawar da Gwamnatin Tarayya wajen cika musu alkawura.
Ogunyemi, wanda ya bayyana hakan a hirasa da wani gidan Talabijin a Abuja ranar laraba, ya ce kasar Ethiopia ta kwashe Farfesoshi sama da 200 kuma har yanzu tana neman kari.
- Za mu ci gaba da yajin aiki har sai bukatunmu sun biya – ASUU
- Yajin aikin ASUU ya sa matasa zaman kashe wando —Sarkin Musulmi
Ya ce, “Muna sane da yadda kasar Ethiopia ta zo Najeriya ta kwashe sama da farfesoshi 200 cikin watannin da suka gabata, kuma har yanzu suna neman kari.
“Saboda haka ban san ko har yanzu gwamnati na da bukatar malamai su cigaba da koyar da yara a jami’oin mu ba, nasan dai ‘yayansu basa cikin jami’oin, hakan yasa suka yi burus da maganar.
“Malamai su ne arzikin duk wata kasa kuma bai kamata a wulakanta su ba,” inji shi.
Ogunyemi ya kara da cewa, barazanar da gwamnati ta ke yi musu na kai kararsu kotu ba zata tsorata su ba,
“Ba masu ilimi ake yi wa irin wannan barazanar ba saboda muna da mafita, kuma babu inda aka taba yin haka aka yi nasara.
“Ina kuma mai tabbatar maka cewar akwai wata jami’ar kudi da ke Yola da ta kwashi malaman jami’oin mu 25 da suka fito daga Arewa maso Gabas. Jami’o’in kudi suna kwasar malaman mu ne saboda a durkusar da su. Ta wannan hanyar ne kadai za su samu sararin habbaka nasun.
ASUU dai ta shiga yajin aikin ne saboda bore ga yunkurin Gwamnati Tarayya na kakaba su cikin tsarin biyan albashi na IPPIS, wanda daga baya suka kirkiri na su tsarin mai lakabin UTAS da hukumar NITDA ke tantacewa a yanzu.