Dan wasan tsakiyar Manchester United Christian Eriksen zai shafe akalla wata uku zuwa hudu yana jinya.
Wannan dai tasgaro da na dan wasan ya gamu da shi na zuwa ne bayan samun rauni a wasan kofin kalubale da suka buga da Reading ranar Asabar.
To amma koci Erik Ten Hag ya yi amanna cewa kulob din na da “yan wasa da za su iya cike gibin da Eriksen zai bari.”
“Ranar karshe abu ne mai wahala ka kawo madadin dan wasa.
“Ba za ka dauki mataki ba bagatatan saboda rauni, to amma kuma muna da ’yan wasa a tsakiya kuma suna da kyau,” In ji Ten Hag.
Dan wasan na Denmark ya buga wa United wasanni 31 a wannan kaka, bayan da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara uku.
Kafin zuwan Eriksen United, ya yi kwallo a Ajax da Tottenham da Inter Milan kafin ya tafi Brentford.
Watakila dan wasan tsakiyar ya iya kaiwa har farkon watan Mayu kafin ya murmure, wato dab da a kare wannan kaka kenan.
Dama United na fuskantar rashin Donny van de Beek, wanda ba zai dawo jinya ba har sai bayan kammala wannan kaka.