✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Enyimba ta kori kocinta Usman Abdallahi

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke garin Aba na Jihar Abia ta kori mai horar da ’yan wasanta, Usman Abdallah. Ita dai Enyimba ita…

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke garin Aba na Jihar Abia ta kori mai horar da ’yan wasanta, Usman Abdallah.

Ita dai Enyimba ita ce ke rike da kambon Gasar Firimiyar Najeriya, wato NPFL.

A safiyar yau Litinin ne kungiyar ta sanar da sallamar kocin, bayan Kungiyar Plateu United ta doke ta da ci 4 da nema a ranar Lahadi.

Yanzu haka Enyimba ce ta 13 a teburin Gasar Firimiyar bana. Ita kuma Plateu United ita ce ke saman tebur.

Ga sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na Tiwita a kasa: