‘Yan sanda sun yi harbe-harbe tare da jefa hayaki mai sa hawaye don tarwatsa wasu matasa da suka tunkari wata ma’ajiya da nufin dasa wawa a kan kayan abinci da Gwamnati ta ajiye na tallafin COVID-19 a Abuja.
‘Yan Kasuwar UTC da ke Area 10 a unguwar Garki sun ji harbe-harbe yayin da mutanen suke kokarin shiga cikin Hukumar Al’adu ta Kasa, suna ikirarin cewa gwamnati ta jibge kayan abincin tallafin COVID-19 a ciki.
Faruwar lamarin ya janyo tsayawar kasuwanci a kasuwar ta UTC inda wasu da dama ba su samu damar cin kasuwar ba a yau.
Aminiya ta zanta da wani da ya tabbatar matsada cewa kasuwa ya zo, shi ba ya cikin masu zanga-zangar #EndSARS amma an tarwatsa su.
Kazalika yayin da aka nemi jin ta bakin wasu daga cikin masu guje-guje don gano dalilin gudun da suke yi, wasunsu sun ce sun zo kasuwa siyayya ne aka tarwatsa su, yayin da neman jin ta bakin masu zanga-zangar ya ci tura.
Alamu dai sun nuna cewa masu zanga-zangar #EndSARS sun ci gaba da yi duk da umarnin da kungiyar da ta jagoranci zanga-zangar tun daga farko ta yi, na kowa ya koma gida ya zauna.