Rundunar ’yan sandan jihar Kano, ta yi nasarar cafke mutane 55 da ake zargi da hannu dumu-dumu da tayar da zaune-tsaye a Unguwar Sabon Gari da ke Kano yayin zanga-zangar EndSARS.
Jami’in hulda da al’umma na Hukumar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020.
- Zanga-zangar EndSARS manufa ce ta yaki da Musulunci – Dokta Gadon Kaya
- Zanga-zangar EndSARS shiri ne na cin mutuncin Buhari – Rashida Mai Sa’a
Ya bayyana cewa ababen zargin da aka cafke, sun shiga hannu ne sakamakon kama su da makamai da suka hada da adduna da wukake da gorori da bindugu da kuma fasa shagunan mutane da diban kayayyakin da ba nasu ba.
DSP Kiyawa ya yi jinjina yayin bayyana irin hadin kai da mutanen Kano suka bayar wajen zakulo bata garin.
Ya kuma ce rundunar ’yan sanda ta jihar ba za ta lamunci duk wasu ayyukan ta’addanci da zanga-zangar da ta wuce gona da iri ba, domin rundunar a shirye ta ke wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar.