Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karyata jita-jitar cewa ya tsere zuwa kasar Faransa a lokacin da aka yi harbe-harbe a Lekki, lokacin zanga-zangar #EndSARS a Legas.
Ya kuma kuma yi watsi da labarin da ke yawo cewa an yi garkuwa da dansa, Seyi Tinubu, a Landan ba gaskiya ba ne.
Tinubu ya bayyana wa manema labarai hakan ne bayan ganawarsa da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Jagoran na APC ya ce yana nan tare da mutanensa a yanayin rikicin da suke ciki.
Ya jajanta wa Sanwo-Olu kan tarzomar da ta faru da kuma asarar rayuka da dukiya da aka yi a Legas, musamman yamutsin da aka yi a Lekki.
Tinubu ya yi tir da harbe-harbe Lekki tare da yi wa matasa fadan kan saba dokar hana fita da gwamnatin jihar ta saka.
Ya bukaci a tuhumi wadanda suka samu harbin bindiga, sannan ya roki matasa a jihar da su daina lalata dukiyoyin gwamnati da na al’umma.