Hukumar shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta dage jarabawan da ta shirya gudanarwa a ranakun Alhamis, Juma’a da Asabar na wannan mako.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Azeez Sani, a cikin wata sanarwa ya ce nan gaba za a gunadar da jarabawan a ranakun 17, 18 da 19 ga Nuwamba mai kamawa.
- ‘Ya kamata Sarkin Musulmi ya hana yin kayan aure’
- Majalisar na rokon a kawo karshen zanga-zangar EndSARS
- EndSARS: An janye ’yan sanda masu kare manyan mutane
NECO ta ce dage ranakun jarabawan ya zama dole saboda yanayin tsaro da ake ciki a sassan Najeriya da ta kai ga rufe makarantu da ma sanya dokar hana fita a wasu jihohi.
Sanarwar ta ce yanayin ba zai ba da damar gudanar da jarabawar ko jigilar kayan gudanarwa cikinn aminci da sauki ba.
Sai dai ta ce tana fatar za ta gudanar da jarabawanta na mako mai zuwa daga ranar Talata.