✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Majalisa ta dage sauraron ra’ayoyin jama’a

Zanga-zanga #EndSARS ta tilasra Kwamitin Majalisa daga taron sauraron ra'ayoyin jama'a

Kwamitin Majalisar Wakilai a Kan harkokin Jiragen Sama ya dage sauraron raayoyin jamaa sakamakon zanga-zangar #EndSARS da ake ci gaba da gudanarwa.

Da farko Majalisar ta tsara fara sauraron ra’ayoyin jama’a kan wasu kudurorinta uku a ranar Talata.

Shugaban Kwamitin, Nnolim Nnaji, ya ce “Dakatar da zaman kwamitin ya zama dole saboda zanga-zangar #EndSARS da ke gudana a kasa”.

Nnaji ya danganta dage zaman sauraron ra’ayoyin jama’ar da matsalolin da wadanda za su halarci taron suke fuskanta sakamakon zanga-zangar.

“Na dade ina amsa wayoyin mutanen da za su halarci taron suna cewa an datse hanyar zuwa filin Jirgin Legas, saboda haka ba za su iya zuwa ba.

“Muna ba da hakurin ga duk wanda dage zaman ya takura ko ya kawo wa cikas”, inji Nnaji, wanda ya ce nan gaba za a sanar da sabon lokaci da za gudanar da taron.

Ya ce manufar jin ra’ayoyin jama’ar shi ne don jama’a su ba da gudunmuwa da shawarwari kan shirye-shiryen sauya wasu daga cikin dokokin jiragen sama na kasa.

Ya ce, kudurin na son a yi wa wasu sassan dokar kafa hukumomi shida gyaran fuska kan wasu abubuwan da Ma’aikatar Jiragen Sama ta kasa ke kula da su.

Hukumomin sun hada da NCAA mai kula da safurin jiragen sama; FAAN mai kula da filayen jiragen sama; NAMA mai kula da sararin samaniya; Kwalejin NCAT mai koyar da tukin jiragen sama; AIB mai binciken hatsarin jiragen sama; da kuma ta NIMET mai kula da hasashen yanayi.

Nnaji ya tunatar da jama’a cewar, Ma’akatar Jirgin Sama wuri ne da ke bukatar canje-canjen harkokin gudanarwa a duk dan tsawon lokacin don harkokin ta su tafi da cigaban zamani.

“Amman an kwashe kusan shekara 14 ba a samu wani sauyi ba duk sauye-sauyen da ke ta faruwa a kasashen duniya.

“Ina kyautata zaton hakan ya sa mahukuntan kasar suka nemi a yi canjin” inji Nnaji.