Kafafen Watsa Labarai na Arewacin Najeriya sun bukaci Shugaba Buhari ya yi azama wurin daidaita al’amura tun kafin kasar ta fada cikin rashin doka da oda.
Kungiyar Mamallakan Kafafen Watsa Labarai na Arewacin Najeriya (NBMOA) ta bayyana kaduwa kan yadda ake sace-sace, kashe-kashe da kone-konen dukiyoyi, har da kafafen watsa labarai, da sunan zanga-zangar EndSARS.
- #EndSARS: Buhari ya ba masu zanga-zanga hakuri
- Zanga-zangar #EndSARS ta rikide zuwa tashin hankali a Kano
Shugaban kungiyar, Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, ya bukaci, “’Yan Najeriya su rungumi tattaunawa sannan muna rokon Shugaba Buhari ya gaggauta yi wa ’yan kasa jawabi da yin kira da a daina salwantar da rayuka da dukiyoyi.
“Muna fargabar sakamakon da furucin ’yan kasa, ’yan siyasa da fitattun mutane game da zanga-zangar da bukatun gyara aikin dan sanda da tsarin shugabancin kasa ke iya haifarwa”, inji shi.
Ramalan ya jaddada aniyar kafafen watsa labarai na Arewacin Najeirya na hana wa miyagu damar amfani da su wurin raba kan jama’a.
“Wajibi ne a wanzar da hadin kan Najeriya da ’yan kasa, masu munanan manufa ba za su samu damar amfani da kafafenmu ba”, inji kungiyar.
Ta kuma bukaci kafafen watsa labarai da su jingine duk wani labari, sako ko sharhi da zai iya ta’azzara barazanar da mulkin dimokuradiyya ke fuskanta a Najeriya.
“Mu kuma za mu yi amfani da labaru da sauran shiryenmu wajen kare tsarin dimokuradiyya da ’yancin fadin albarkacin baki tare da yada bukatar samun shugabanci na gari, adalci da gaskiya domin samar da yarda a tsakaninin ’yan kasa.