Duba da yadda zanga zangar kin jin rundunar tsaro ta SARS ta yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyin al’umma, Gwamnatin jihar Filato a ranar Talata ta sanya dokar hana fita, ta tsawon awa 24 har sai baba ta gani.
Gwamnan jihar Simon Lalong ne, ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatarwa al’ummar jihar,a Yammacin ranar Talata.
- #EndSARS: Shugaba Buhari ya gana da Ministan tsaro
- Zanga-zangar #EndSARS ta rikide zuwa tashin hankali a Kano
Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda aka fara wannan zanga zanga ta lumana, amma daga baya wasu bata gari, suka yi amfani da wannan dama suka farma mutanen da basu ji basu gani ba.
Gwamnan ya ce wannan zanga zanga, ta juya zuwa wani mummunan mataki a ranar talatar nan, inda aka kona motoci tare da lalata dukiyoyin jama’a a hanyar Ahmadu Bello da ke Jos da kasuwar Taminus da kuma kone-kone a kan hanyar Gyero da ke garin Bukur tare da salwantar rayukan mutum uku.
“Ganin wannan hali da aka shiga, ya sanya muka kira taron majalisar tsaro ta jihar nan, don duba matakan da zamu dauka, na dakatar da wannan mummunan al’amari.
“Don haka gwamnati ta dauki wannan mataki na sanya wannan doka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.’’
“Saboda haka daga yanzu mun sanya wannan doka ta hana fita ta tsawon awa 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, daga karfe 8 na daren yau, har sai yadda hali ya yi.’’
Gwamnan ya ce saboda haka an dakatar da komai na harkokin yau da kullum, a wuraren da aka sanya wannan doka inda ya umarci jami’an tsaro su tabbatar jama’a sun bi umarnin wannan doka.