✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: An shawarci ‘yan kasuwa su kauracewa zuwa Legas 

Yayin da zanga-zangar #EndSARS ke kara kazancewa, an shawarci ‘yan kasuwa daga Arewacin Najeriya da su dakata da zuwa Jihar Legas domin kasuwanci. Babban limamin…

Yayin da zanga-zangar #EndSARS ke kara kazancewa, an shawarci ‘yan kasuwa daga Arewacin Najeriya da su dakata da zuwa Jihar Legas domin kasuwanci.
Babban limamin masallacin Juma’a na Sultan Bello dake Kaduna, Sheikh Muhammed Suleiman Adam Abubakar shine ya yi gargadin yayin hudubar sallar Juma’a.
Sheikh Abubakar ya ce akwai gagarumin hatsari ga dukkan ‘yan kasuwar dake yankin Arewaci da suke safarar kaya daga yankin zuwa kudu ko su saro daga kudu zuwa arewa musanman jihar Legas da ta yi kaurin suna a zanga-zangar.
Babban limaman ya ci gaba da cewa lalata kayan gwamnati da ba kamfanoni masu zaman kansu da masu zanga-zangar suka yi abun damuwa ne kwarai da gaske.
Daga nan sai ya kira da gwamnatin tarayya da ta yi kokarin ganin ta biya diyyar duk wata barma da masu zanga-zangar suka yi ga wadanda suka rasa dukiyoyinsu.