Kotu ta sanya ranar Talata 15 ga watan Agusta da muke ciki a matsayin ranar sauraron bukata dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke neman hana gwamnati gurfanar da shi.
Kotun ta sanar da haka ne a zamanta na safiyar Juma’a, inda Emefiele ya bukaci ta yi watsi da zargin da hukumar DSS ke masa na mallakar haramtattun makamai.
- ‘Farashin gas din girki zai iya tashi a Najeriya mako mai zuwa’
- NAJERIYA A YAU: Ƙuncin Da Ake Ciki A Kan Iyakar Najeriya Da Nijar
Alkalin kotun, Nicholas Oweibo, ya ce lokacin da aka sanya zai ba da dama ga bangarorin su shirya martaninsu ga juna a shari’ar ta Emefiele da ke tsare a hannun DSS tun ranar 10 ga watan Yuni.
A ranar ce Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Legas za ta saurari bukatar hukumar tsaro ta DSS da ke tsare da Emefiele na neman kotun ta janye belinsa da ta bayar.
A zaman kotun na baya ne ta ba da belin Emefiele a kan Naira miliyan 20 da mutum biyu da za su tsaya matsa, inda ta bukaci a tsare shi a gidan yari sai ya cika sharuddan.
A yayin da ake shirin tafiya da shi gidan yari ne jami’an hukumar DSS suka murkushe takwarorinsu na hukumar gidajen yari a harabar kotu, suka yi awon gaba da shi, wanda hakan ya ja musu Allah-wadai.
Hukumar dai ta nesanta kanta da gaban kai da ta ce jami’anta suka yi, tare da alkawarin daukar mataki a kan duk wanda ta samu da laifin saba ka’idar aiki.
Sai dai zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gareta game da inda aka kwana.