✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Emefiele ya maka INEC a gaban kotu kan yunkurin hana shi tsayawa takara

Emefiele dai ya maka INEC ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya maka Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) a gaban kotu kan yunkurin hana shi tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.

Emefiele dai ya maka INEC ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ahmed Mohammed ne dai zai jagoranci shari’ar.

A karar dai da lauyan shi, Mike Ozekhome, ya shigar, Emefiele ya roki kotun ta hana INEC da Babban Lauyan Gwamnati daga dakatar da shi shiga zabe, dogaro da sashe na 84 (12) na Dokar Zabe ta 2022.

Gwamnan bankin ya kuma nemi kotun da ta yi dogaro da sashe na 137(1) da na 318 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da ya bukaci mai rike da mukamin siyasa ya sauka daga mukaminsa kwana 30 kafin ranar Zaben Shugaban Kasa, a maimakon na Dokar Zaben.

A makon da ya gabata ne dai Gwamnan Babban Bankin ya sayi fom din takarar Shugaban Kasa kan Naira miliyan 100 karkashin jam’iyyar.