✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Twitter na asarar N3bn a kullum —Elon Musk

Twitter ya shiga rudani bayan asarar Dala miliyan 8 a kullum sakamakon kaurace masa da masu talla suka yi.

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya shiga rudani sakamakon tafka asarar Dala miliyan hudu (kimanin Naira biliyan uku) a kullum bayan kaurace masa da kamfanonin tallace-tallace suka yi.

A ranar Juma’a ne sabon mai kamfanin kuma mai kudin duniya, Elon Musk, ya sallami rabin ma’aikatan kamfanin, mako guda bayan ya saye shi Dala biliyan 44.

Tun ranar Juma’a da aka kammala cinikin Elon Musk ya sallami manyan darkatoci sannan ya karbe ragamar kamfanin.

Da Jama’a da zagayo kuma, Twitter mai ma’aikata 7,500 a fadin duniya, ya tura wa kusan rabinsu takardun sallama, lamarin da ya shammata tare da fusata yawancinsu.

Daga cikinsu, Daraktar Hulda da Jama’ar Twitter a Amurka da Kanada, Michele Austin, ta ce, “Na wayi gari da samun sakon sallama daga Twitter. Wannan abin takaici da me ya yi kama. Na kasa yarda!”

Rage ma’aikata ya zama dole —Musk

Sallamar ma’aikatan na da daga cikin hanyoyin da attajirin ya dauka domin biyan kudin kamfanin gami da sayar da hannayen jarin Dala 15.5bn a kamfaninsa na Tesla da kekera motoci masu amfani da lantarki.

Wani ma’aikaci da aka sallama, ya ce, “Wannan rashin imani ne… Su dai damuwarsu su rage kudaden da suke kashewa, to kowace hanya.”

Gabanin sanar da sallamar a ranar Juma’a, Elon Musk ya wallafa cewa, “Rage ma’aikata ya zama dole, saboda kamfanin na asarar Dala miliyan hudu a kullum.”

Tun kafin sallamar ma’aikatan a fadin duniya, Twitter ya tura musu sakon imel cewa su zauna a gidajensu su jira sako game da makomarsu a kamfanin.

Kamfanin dillanci labarai na Reuters a ce raga ma’aikatan ya kunshi rufe wasu sassa na kamfanin, ciki bar da na wasu bincike kan dabi’un masu amfani da kafar.

Ma’aikatan da suka rage sun ce a halin yanzu, kamfanin yana lafta musu aiki, tare da kawo jami’ai daga Telsa su lura da wasu ayyukan da ke gudana.

Rahotanni sun gano cewa ana bin Musk bashin kudin ruwan Dala biliyan daya a shekara daga cinikin da ya nemi ya fasawa a watan Afrilu.

Mutum 1m sun bar Twitter a mako 1

Twitter ya shahara a wajen fitattun mutane da masu fada-a-duniya, amma har yanzu matakan samun kudaden shigarsa bai yi nasara ba, kamar irin su Facebook da Instagram da TikTok wajen samun sabbin masu amfani da kafarsa.

Wani abin da ke nuna tsugune ba ta kare ba, shi ne kusan mutum miliyan daya sun daina amfani da shi daga lokacin da kamfanin ya koma mallakin Musk.

Cibiyar Bot Sentinel, mai lura da alkaluman masu amfani da Twitter ta ce mutum 875,000 sun rufe shafukansu na Twitter daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 1 ga Nuwamba, 2022, sama da 500,000 kuma sun daina amfani da su.

Farfado da kudaden shiga?

Yanzu haka mai Musk na neman hanoyin habaka kudaden shigar Twitter, ciki har da sanya Dala takwas a wata ga duk shafin da ke alamar inganci a kafar.

Hakan na daga cikin matakan da ya dauka na rage barazanar nakasun kudaden shiga daga tallace-tallace wadanda kamfanin ya fi dogara da su.

Wannan kuma na zuwa ne bayan manyan masu bai wa kamfanin talla sun dakatar, saboda hallayar sabon mai kamfanin na barin mutane su yi duk abin da suka ga dama.

Tsaka mai wuya

A ranar Juma’a Alon Musuk ya koka game da “kankancewar kudaden shigar Twitter,” wanda ya dora laifin a kan kungiyoyin fafutika da ke matsin lamaba ga masu ba da tallace-tallace.

A cewarsa, “Mun yi duk iyawarmu don dadada wa ’yan gwagwarmayar. Amma komai ya lalace! So suke su rusa damar fadin albarkcin baki a Amurka.”

Kalaman nasa na da nasaba da zmaan da kungiyoyin suka yi da shi, inda suka bayyana damuwa cewa Twitter zai bude kofar kalaman tsana, mako guda kafin zabin rabin zango a kasar.

Amma attajirin ya ce kafar ba za ta zama fagin ‘hayaniya ba’, sai dai kuma tun da kamfanin ya koma hannunsa, shi da kansa ya yi ta tura sako da ke zargin makirci a harin da aka kai wa mijin Nancy Pelosi, Shugabar Majalisar Dokokin Amurka.

‘Twitter a hannun Musk barazana ce’

Babbar Daraktan kamfanin Accountable Tech, Nicole Gill ta ce, “Muna ganin yadda ake kokarin rusa daya daga manyan kafofin sadarwa na duniya.

“Elon Musk rikitaccen biloniya ne da ba shi da kwarewar gudanar da irin wannan kafa.”

Nicole Gill tana daga cikin jagororin gamayyar kungiyoyin kare hakki guda 60 wadanda a ranar Juma’a suka yi kira ga masu bayar da tallace-tallace su kaurace wa kamfanin na Elon Musk.

Shugaban Kungiyar Kare Hakii ta NAACP, Derrick Johnson, ya ce, “Shirme ne, kuma babbar barazana ce ga tsarin dimokuradiyya wani kamfanin tallace-tallace ya bayar da kudinsa ga kafar da ke yada maganganun tsana, kirkirarrun maganganu da kuma taurin kai a lokacin zabe.

“Idan ba daukar matakan tabbatar da aminci aka yi ba, muna kira ga kamfanoni da su daina bai wa Twitter talla,” in ji shi.

Shugaban sashen tsare aminci da martabar kamfanin, Yoel Roth, ya yi kokarin shawo kan kungiyoyin, da cewa kashi 15% na jami’an sashen sashen aka sallami,  idan aka kwatanta da kusan rabin ma’aikatan da aka sallama a fadin kamfanin.

Saboda haka, “Tushen tabbatar da inganci bai samu wata gagarumar nakasu ba,” in ji sakon da ya wallafa a Twitter.