Sabon mamallakin kamfanin Twitter, Elon Musk, ya mayar wa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump da shafinsa na Twitter bayan kimanin shekara biyu da rufe shi.
Kamfanin Twitter a baya ya zargi tsohon Shugaban da laifin tunzura magoya bayansa wanda hakan ta kai ga tashin hankali a Amurka.
- Mutumin da ya taso a Najeriya ya auri ’yar Donald Trump
- Donald Trump ya kaddamar da takararsa ta sake neman Shugabancin Amurka
An dawo wa da Trump shafinsa ne a ranar Asabar, bayan da Elon Musk ya yi wata ‘yar kwarya-kwaryar jin ra’ayin jama’a na ko a dawo masa da shafin ko kuma a’a.
Mutane sama da miliyan 15 ne suka kada kuri’ar jin ra’ayin, a inda suka amsa tambayar shin ya kamata a dawo masa da shafin na sa ko a’a, a inda masu rinjaye suka bayar da amsar eh, da suka yi rinjaye da kaso 51.8 cikin 100.
“Jama’a sun bayyana ra’ayinsu. Za mu dawo wa da Trump shafinsa,” a cewar wani sako da Musk ya wallafa shafin nasa na Twitter.
Kafin nan, a ranar Asabar Trump ya bayyana cewa ba shi da aniyar dawowa dandalin sada zumuntar na Twitter.
“Hakan ba shi da wani amfani,” inji tsohin Shugaban, a wata amsa da ya bayar ta hoton bidiyo a wata tambaya da aka yi masa, kan ko zai ci gaba da amfani shafin na sa na Twitter idan an dawo masa da shi.
Trimp ya ce zai ci gaba ba ne da amfani da sabon dandalin da ya kirkira, ya kuma kira shi da sunan ‘Gaskiyar mu’amala’.