Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai yiyuwar sake sanya dokar zaman gida a jihar sakamakon samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19.
Mai taimaka wa gwamnan a kafofin watsa labarai, Abdallah Yunus Abdallah, ya ce kare dukiyoyi da rayukan al’umar jihar wajibi a kan gwamnan, shi ya sa ya yi wannan jan kunnen.
- Badakalar fansho: Maina ya sake sumewa a kotu
- Buratai ya soke taron shekara bayan soja ya kamu da COVID-19
- Aikin Hajj: NAHCON ta fadada Tsarin Adashin Gata
Abdallah, ya ce tabbas gwamnan zai sake sanya dokar zaman gida muddin jama’a suka ki kiyaye hanyoyin hana yaduwar cutar aka kuma ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da ita.
“Yanzu yaki da cutar aiki ne da ya rataya a kan kowa ba iya gwamnati ba; zama wajibi a kan mutane su kula da kansu da dakile cutar”, inji shi.