Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sha suka bayan ya nemi a biya N500,000 kafin a gudanar da Sallar Idi a Filin Idi da ke Dandalin Murtala Muhammad.
Gwamnatin El-Rufai ta nemi a biya kudin ne cikin kwana biyar ta hannun Hukumar Kasuwannin Jihar Kaduna, bayan a ranar 6 ga watan Yuli, Masallacin Tijjaniyya da ke Titin Doka a garin Kaduna ya rubuta mata takardar neman izinin gudanar da Sallar Idin Babbar Sallah a filin.
- Babbar Sallah: Hukumar NSCDC ta tura jami’ai 30,000 domin sintiri
- An harbi tsohon fira ministan Japan Shinzo Abe a bainar jama’a
Wasikar amsar da hukumar ta aike wa masallacin ya ce, “Ku tuna cewa tun a shekarar 2020 muke tattaunawa kan wannan batun.
“Saboda haka wannan ne karo na karshe da za mu bari ku yi Sallar Idi a dandalin; Don haka ku biya N500,000 kacal.”
Sakataren masallacin idin, Malam Sunusi Surajo, ya tabbatar wa Aminiya cewa gwamnatin ta bukaci su biya N500,000 kafin gudanar da Sallar Idi.
An dai shafe kimanin shekara 50 mabiya Darikar Tijjaniyya suna Sallar Idi a filin da ke kwaryar garin Kaduna.
El-Rufai ya yi amai ya lashe
Tun bayar bullar wasikar a kafofin intanet al’ummar Musulmi ke ta sukar Gwamnatin El-Rufai bisa wannan mataki da ta dauka.
Wakilinmuya gano cewa daga baya ta janye batun neman kudin, bayan sukar da matakin ya ja mata.
Malam Sunusi Surajo ya ce, “Gaskiya ne sun bukaci mu biya N500,000 kafin mu yi amfani da filin idin.
“Amma mun tattauna da wakilan gwamnati kuma ta janye maganar, ta ce mu ci gaba da amfani da wurin ba sai mun biya ba.”
Wani malami mai gabatar da wa’azi a filin idin, Shaikh Haliru Maraya, ya bayyana janye matakin a matsayin borin kunya.
Sheikh Halliru Maraya ya ce Musulmi sun cika da mamakin matakin domin an fi shekara 50 ana gudanar da Sallar Idi a wurin.
Tsohon Daraktan Hukumar Addinai ta Jihar Kaduna, Shaikh Jamil Albany, ya musanta rade-radin da ke cewa sai da aka sanya kudin a asusun gwamnatin jihar kafin ta janye maganar.
Wata wasikar da Hukumar Kasuwannin Jihar Kaduna ta aike a ranar Alhamis ta ce El-Rufai ya amince a daga wa masallacin kafa.
“Muna farin cikin sanar da ku cewa gwamna ya yanke shawarar janye kudin amfani da filin Idin,” in ji Manajan Daraktan hukumar, Tamar Nandul.