Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanyan a kananan hukumomin Kaura da Jema’a sakamakon tashin-tashina da aka yi a yankunan.
Hukuncin sassauta dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, ya biyo bayan rahoton fara daidaituwar al’amura a yankunan da jami’an tsaro suka gabatar wa gwamnatin jihar.
- Buhari ya gana da Tinubu da Bisi Akande gabanin taron APC
- NAJERIYA A YAU: ’Yan sandan da gaskiyarsu ta girgiza jama’a
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
A cewarsa an cimma matsayar yin zirga-zirga daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a yankunan, kana dokar ta ci gaba daga 6 na yamma zuwa 6 na safiya a kullum.
Kazalika, gwamnatin jihar ta yi barazanar sake dawo da dokar matukar mazauna yankunan suke bijirewa dokokin da aka shimfida musu.
Har wa yau, za a ci gaba da sanya ido kan yadda al’amura ke wakana a yankunan, don tabbatar da ba a sake samun tashin-tashina ba.