Gwamnatin Jihar Kaduna ta sasauta dokar hana fita na awa 24 a Kananan Hukumomin Jema’a da Kaura da yankin Kudancin jihar da aka sanya a makonni biyu da suka wuce sakamakon hare-haren da aka kai a yankin Masarautar Zikpak.
Dokar da aka sassauta daga 6.00 na safe zuwa 6.00 na yamma kuma ta fara aiki a ranar alhamis, bayan sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar.
Ya ce daukar matakin ya biyo bayan rahoton jami’an tsaro bayan sun bibiyi lamarin kuma suka bayar da shawarar rage dokar.
“A dalilin haka ne muka sassauta dokar da za ta koma daga karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma a kullum”, inji sanarwar
Sai dai sassaucin bai shafi kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf ba, inda ya ce ana ci gaba da duba yiwuwar hakan nan gaba bayan lura da yadda hali yayi.
An sanya dokar hana fita na awa 24 ne a kananan hukumomin Jema’a da Kaura bayan kai harin ranar Jumma’a, 24 ga watan Yuli a wasu yankuna na kananan hukumomin biyu.
A kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf, inda sabon rikicin Kudancin Kaduna ya farfado, an sanya dokar hana fita ne a ranar 11 ga watan Yuni, inda suke tunkarar makonni goma a cikin dokar.
Jama’a da dama da Aminiya ta zanta da su a yankunan kananan hukumomin Jema’a da Kaura sun bayyana farin cikinsu da rage dokar, sakamakon halin da suka shiga na kuncin rayuwa.
Sun ce a wannan shekarar sun tsinci kansu cikin wani hali mai matukar wahala da kuncin rayuwa, kasantuwar ba su gama farfadowa daga kullen da suka fito da aka sanya a dalilin coronavirus ba; ga kuma tsadar rayuwa da rashin isasshen kudi, kuma aka sake jefa su cikin dokar hana zirga-zirga na awa 24.
“Gaskiya mun ji dadin sassauta wannan dokar, babu abun da ya kai zaman lafiya dadi”, Inji wasu da Aminiya ta zanta da su.