✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya sassauta dokar hana fita a Kaduna

An dauki matakin hakan ne biyo bayan shawarwarin da Hukumomin Tsaro suka ba Gwamnati.

Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Mallam Nasir El-Rufai, ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta shimfida a kokarinta na dakile yunkurin mutane na dasa wawa a kan rumbunan ajiyar abinci.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Litinin da cewa sabuwar dokar hana fita wadda za ta fara aiki daga gobe Talata za ta fara ne da karfe 4:00 na Yamma zuwa 6:00 na safe.

Sai dai ya ce ba a yi sassauci a kananan Hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun ba, inda ya ce dokar tana nan daram ta awa 24 kamar yadda aka shimfida a baya.

Cikin rahoto da jaridar BBC ta wallafa, kwamishinan ya ce an dauki matakin hakan ne biyo bayan shawarwarin da Hukumomin Tsaro na Jihar suka ba Gwamnati.

Ya yi karin haske da cewa ba a sassauta dokar a Chikun da kuma Kaduna ta Kudu ba sakamakon yadda har yanzu al’umma ke ci gaba da satar kayan abinci, wanda a sanadiyar haka ne aka umarci mazauna yankunan su ci gaba da zama a gida.