✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya sassauta dokar hana fita a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita a fadin jihar, inda a yanzu ta koma daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita a fadin jihar, inda a yanzu ta koma daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma, domin bai wa al’umma damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar yadda aka saba.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya yi karin bayani game da sassauta dokar a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa bayan zaman da gwamnati ta yi da jami’an tsaro a kan yanayin tsaro a jihar, hakan ya basu damar sassauta dokar a fadin jihar baki daya.

Aruwan ya ce “Daga ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2020, mutanen jihar na da damar ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar yadda suka saba daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.”

“An hana gudanar da zirga-zirga da daddare a yayin da dokar za ta fara aiki daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe,” a cewar Aruwan.

Sanarwa ta ce, ana kira da jama’ar jihar Kaduna da su bi umarnin doka, su kuma sanya ido da kai rahoton duk wani abu da basu gamsu da shi ba, yayin da kuma aka bukaci su bawa dukkan hukumomin tsaro hadin kai domin sauke nauyin da rataya a wuyansu.